Masawud Mohammed
Masawud Mohammed | |||||
---|---|---|---|---|---|
7 ga Janairu, 2017 - District: Pru West Constituency (en) Election: 2016 Ghanaian general election (en)
7 ga Janairu, 2013 - 6 ga Janairu, 2017 District: Pru West Constituency (en) Election: 2012 Ghanaian general election (en) | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | 1 ga Afirilu, 1971 (53 shekaru) | ||||
ƙasa | Ghana | ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
University of Cape Coast Master of Education (en) : Ilimin halin dan Adam University of Cape Coast Bachelor of Education (en) : Ilimin halin dan Adam | ||||
Harsuna | Turanci | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa da consultant (en) | ||||
Imani | |||||
Addini | Musulmi | ||||
Jam'iyar siyasa | National Democratic Congress (en) |
Masawud Mohammed (an haife shi 1 Afrilu 1971), ɗan siyasa ne na ƙasar Ghana kuma ɗan majalisa na bakwai na jamhuriya ta huɗu ta Ghana mai wakiltar mazabar Pru ta Yamma a yankin Bono ta Gabas a karkashin jam'iyyar National Democratic Congress.[1][2]
Shekarun farko da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Mohammed a ranar 1, ga Afrilu 1971, a Prang a yankin Bono. Ya halarci Jami'ar Cape Coast kuma ya kammala karatun digiri da digiri na biyu a fannin Ilimi.[2][3]
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Mohammed ya kasance dan majalisa mai wakiltar Pru West Constituency. Kafin wannan aiki ya yi aiki a matsayin malami a Kwalejin Ilimi ta Atebubu sannan ya zama shugaban gundumar Pru.[2][3]
Siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Ya fara zama dan majalisa a shekarar 2013, mai wakiltar mazabar Pru West. A shekarar 2016, ya sake tsayawa takarar kujerar a babban zaben 2016, kuma ya yi nasara. Ya samu kuri'u 10,740. Wanda ke wakiltar kashi 49.66% , na yawan kuri'un da aka kada, don haka ya doke sauran 'yan takarar da suka hada da Stephen Pambiin Jalulah da Eric Kwabena Asamoah da Akurugu Zakarai Atiah.[2][4]
Rayuwa ta sirri
[gyara sashe | gyara masomin]Mohammed musulmi ne. Yana da aure da ‘ya’ya hudu.[2]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Hon. Masawud Mohammed". Parliament of Ghana. Retrieved 3 August 2020.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 2.3 2.4 "Ghana MPs - MP Details - Mohammed, Alhaji Masawud". www.ghanamps.com. Retrieved 2020-02-01.
- ↑ 3.0 3.1 "Ghana Parliament member Masawud Mohammed (Alhaji)". www.ghanaweb.com. Retrieved 2020-02-01.[permanent dead link]
- ↑ FM, Peace. "Ghana Election 2016 Results - Pru West Constituency". Ghana Elections - Peace FM. Retrieved 2020-02-01.