Metapontum
Metapontum | ||||
---|---|---|---|---|
Greek colony (en) , archaeological site (en) da polis (en) | ||||
Bayanai | ||||
Suna a harshen gida | Μεταπόντιον | |||
Ƙasa | Italiya | |||
Kasancewa a yanki na lokaci | UTC+01:00 da UTC+02:00 (en) | |||
Heritage designation (en) | Italian national heritage (en) | |||
Email address (en) | mailto:drm-bas.museometaponto@beniculturali.it | |||
Shafin yanar gizo | museometaponto.beniculturali.it… | |||
Wuri | ||||
| ||||
Ƙasa | Italiya | |||
Region of Italy (en) | Basilicata (en) | |||
Province of Italy (en) | province of Matera (en) | |||
Commune of Italy (en) | Bernalda (en) |
Metapontum ko Metapontium (Ancient Greek) wani muhimmin birni ne a Magna Graecia, wanda ke kan gabar tekun Tarentum, tsakanin kogin Bradanus da Casuentus ( Basento na yau). Tana da nisan kusan 20 km daga Heraclea sanan kuma kilomita 40 daga Tarentum. Burbushin Metapontum na nan a yankin frazione na Metaponto, a cikin alkaryar Bernalda, a lardin Matera, yankin Basilicata, kasar Italiya.
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Kafa ta
[gyara sashe | gyara masomin]Duk da cewa Metapontum ta kasance yankin mulkin mallaka ta Achaean ta Girka na da,[1] al'adu da dama sun samo asalinsu da tarihinta na farko. Strabo[2] da Solinus[3] sun nuna asalin kafuwarta da birnin Pylos, a matsayin wani bangare na wadanda suka bi Nestor zuwa Troy. Justin ya nuna mana cewa, Epeius na Phocis ne ya kafa ta, a wani hujja da mutanen suka tabbatar a wurin bauta na Minerva, da kayan aiki wanda jarumin yayi amfani da su wajen kera Dokin Trojan.[4] Wani labarin gargajiya wanda Ephorus ya bayar,[5] ya alakanta asalin tarihinta da Phocis, sannan ya kira Daulius, wani azzalumin shugaba na Crissa kusa da Delphi, matsayin wanda ya kirkire ta. Sauran masana sun alakanta tarihin kafuwarta da wasu lokuta na daban.