Milka Irene

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Milka Irene
Rayuwa
Haihuwa Buwenge (en) Fassara, 1989 (34/35 shekaru)
ƙasa Uganda
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a Jarumi

Milka Irene Soobya ta kasance yar'fim din kasar Uganda ce kuma yar'siyasa wacce ta shahara sanadiyar fitowarta amatsayin Monica acikin shirin NTV Uganda jerin diramomin Deception da kuma Fifi Aripa a Power of Legacy. Ta nemi takarar zama mamba a Majalisar Jinja bayan baiwa Jinja matsayin zama birni a kasar.[1][2]

Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Soobya ta fara aikin shirin fim ne da fitowa a kananan vidiyoyi na jerin shirye-shirye na kasar Kenya Makutano Junction wanda Philip Luswata ya gabatar da ita, wanda daya ne daga cikin marubutan shirin. Sai dai ta samu shahara asanda ta fito a jagoran mataki Monica a NTV Uganda jerin drama Deception daha 2013 zuwa 2016.[3][4] Daga baya tayi aiki a Akpor Otebele fim din da yayi darekta, The Rungu Girls, Honeymoon is Exaggerated, Christmas in Kampala da kuma Taxi 24. A shekarar 2018, ta fito acikin shirin Power of Legacy amatsayin Fifi Aripa, a freeloader da Rachael's (Tania Shakira Kankindi) babbar kawa.[5]

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

A 2020, Soobya ta shiga siyasa ka'in dana na'in inda ta nemi zama mamba a Majalisar kasarta don wakiltar Birnin Jinja a karkashin jam'iyyar National Resistance Movement bayan ayyana Jinja amatsayin birni maicin gashin kansa.[6]

Fina-finai[gyara sashe | gyara masomin]

Shekara Film/TV Series Mataki Bayanai
2013 -2016 Deception" Monica Lead role
2016 Christmas in Kampala Christmas film
The Rungu Girls
Honeymoon is so Exaggerated
Taxie 24 ug
2016 - to-date Family Affairs Herself – Co-host Talk Show on Spark TV
2018 Power of Legacy Fifi Arripa Television series, main cast

Rayuwarta[gyara sashe | gyara masomin]

Soobya an haife ta ne a Jinja daga gidan mahaifin ta Lt. Colonel Samuel Kafude Ngobi da Capt. Namutebi Agnes Mbuga, wadanda dukkanin su sojojin UPDF ne. Ta yi karatun ta a Mbogo High School na O Level, da Mariam High School na A-Level da kuma Jami'ar Kyambogo inda ta kammala da digiri a fannin Procurement and Logistics Management.[7]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Milka on being Monica in 'Deception'". The Independent. Retrieved 26 August 2020.
  2. Baike, Prisca. "Deception's Irene Milka tithes faithfully". The Observer. Archived from the original on 2 November 2020. Retrieved 26 August 2020.
  3. Batte, Edgar. "Irene Milka: Deception's leading lady". Sqoop. Retrieved 26 August 2020.
  4. Male, Marvin. "God's word will bring a turn-around in your life, says actress Irene Milka". Uganda Christian News. Retrieved 26 August 2020.
  5. Gachie. "Irene Milka Biography, Music, Family and Awards". Africa Mania. Retrieved 26 August 2020.[permanent dead link]
  6. Kazungu, Daniel. "RACE TO 2021 POLLS: Who will be Jinja city's first Women representative?". PML Daily. Retrieved 26 August 2020.
  7. "Deception TV Series Star Milka Irene (Monica) Graduates From Campus". Big Eye. Retrieved 26 August 2020.[permanent dead link]