Milton Obote
![]() | |||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
![]() | |||||||||||
17 Disamba 1980 - 27 ga Yuli, 1985 ← Paulo Muwanga (mul) ![]() ![]()
Disamba 1980 - ga Yuli, 1985 ← Lawrence Sebalu (en) ![]() ![]()
1980 - 1985 ← Otema Allimadi (en) ![]() ![]()
2 ga Maris, 1966 - 25 ga Janairu, 1971 ← Muteesa II (en) ![]()
30 ga Afirilu, 1962 - 15 ga Afirilu, 1966 ← Benedicto Kiwanuka (en) ![]() | |||||||||||
Rayuwa | |||||||||||
Cikakken suna | Apollo Milton Opeto Obote | ||||||||||
Haihuwa |
Apac (en) ![]() | ||||||||||
ƙasa | Uganda | ||||||||||
Mutuwa | Johannesburg, 10 Oktoba 2005 | ||||||||||
Makwanci |
Akokoro (en) ![]() | ||||||||||
Yanayin mutuwa |
Sababi na ainihi (kidney failure (en) ![]() | ||||||||||
Ƴan uwa | |||||||||||
Abokiyar zama |
Miria Obote (en) ![]() | ||||||||||
Karatu | |||||||||||
Makaranta |
Jami'ar Makerere Adams College (en) ![]() Busoga College (en) ![]() | ||||||||||
Harsuna | Turanci | ||||||||||
Sana'a | |||||||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||||||
Aikin soja | |||||||||||
Fannin soja |
Uganda People's Defence Force (en) ![]() | ||||||||||
Imani | |||||||||||
Jam'iyar siyasa |
Uganda People's Congress (en) ![]() |
Apollo Milton Obote (28 Disamba 1925 - 10 Oktoba 2005) ɗan siyasar kasar Uganda ne wanda ya yi aiki a matsayin Firayim Minista na biyu na kasar daga 1962 zuwa 1966 kuma shugaban Uganda na biyu daga 1966 zuwa 1971 kuma daga baya daga 1980 zuwa 1985.
Ya yi karatu a Kwalejin Busoga da Jami'ar Makerere. A shekarar 1956, ya shiga Majalisar Dokokin Kasa ta Uganda (UNC) sannan daga baya ya barta ta hanyar kafa Majalisar Jama'ar Uganda (UPC) a shekarar 1960. Bayan Uganda ta sami 'yancin kai daga Mulkin mallaka na Burtaniya a shekarar 1962, an rantsar da Obote a matsayin Firayim Minista a cikin hadin gwiwa tare da Kabaka Yekka, wanda aka nada shugabansu Mutesa II a matsayin shugaban kasa. Daliliin rikici da Mutesa a kan zaben raba gardama na kananan hukumomi na 1964, Obote ya hambarar da shi a 1966 kuma ya ayyana kansa shugaban kasa, ya kafa mulkin kama karya tare da UPC a matsayin jam'iyyar hukuma a shekarar 1969. A matsayinsa na shugaban kasa, Obote ya aiwatar da wasu manufofi, wanda a karkashinsa kasar ta sha wahala daga cin hanci da rashawa da karancin abinci.