Jump to content

Mina Kiá

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mina Kiá
Asali
Lokacin bugawa 2017
Asalin harshe Portuguese language
Ƙasar asali Sao Tome da Prinsipe
Characteristics
Genre (en) Fassara Fiction (Almara)
During 45 Dakika
Direction and screenplay
Darekta Katya Aragão (en) Fassara
External links

Mina Kiá ( yan aikin gida) wani ɗan gajeren fim ɗin wasan kwaikwayo ne na shekarar 2017 daga São Tomé da Principe, babban darakta na Katya Aragão . Fim din na bayar da labarin irin wahalhalun da ƴan mata suke fuskanta a birnin Sao Tomé. Fim ɗin ya ƙunshi Ana Pinheiro a matsayin jagora shirin. Ƙarin mahalarta sun haɗa da Ely Patrícia, Marilene Mandinga, Ayuba do Mocho, da Djamila Costa.

An zaɓi fim ɗin don nunawa a bukukuwan fina-finai na duniya da yawa, galibi na harshen Portuguese, ciki har da Kugoma - Dandalin Fim na Mozambique a Maputo,[1] São Tomé and Principe International Film Festival, FESTIN, bikin fina-finai na harshen Portuguese na duniya,[2] bikin fina-finai na mata na duniya Porto Femme,[3] bikin fina-finai na Cape Verde na Turai, da makon fina-finan Afirka a Angola House a Brazil.

A ranar tunawa da karo na 29th na Yarjejeniya kan 'Yancin Yara, an nuna fim ɗin a wani haɗin gwiwar Alliance Française da UNICEF, a watan Nuwamba 23, 2018, kuma an watsa shi a gidan talabijin na ƙasa da ƙasa RTF a ranar 3 ga watan Nuwamba, 2018.

  1. "Maputo hosts cinema festival from Portuguese-speaking countries". Club of Mozambique. September 28, 2019. Retrieved March 2, 2019.
  2. "Mina Kiá". Cinema São Jorge. Archived from the original on October 10, 2021. Retrieved March 2, 2019.
  3. "PORTO FEMME SESSIONS #10". Porto Femme. March 29, 2018. Archived from the original on April 28, 2019. Retrieved March 2, 2019.

Hanyoyin Hadi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]