Miriam Rodriguez Martinez

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Simpleicons Interface user-outline.svg Miriam Rodriguez Martinez
Rayuwa
Haihuwa 5 ga Faburairu, 1960
ƙasa Mexico
Mutuwa San Fernando (en) Fassara, 10 Mayu 2017
Sana'a
Sana'a Mai kare ƴancin ɗan'adam

Miriam Rodriguez Martinez (an haife ta 5 ga watan Febrairun shekarar 1960 -ta mutu a ranar 10 ga watan Mayun shekarar 2017, San Fernando, Tamaulipas, Mexico), ta kasance ƴar gwagwarmayar kare hakƙin ɗan adam ce daga Mexico. Ta zama mahaifiya budurwa wanda haka ƴan'jaridu ke masu laƙabi bayan sace ƴarta da kashe ta da akayi. Ƴan bindiga sun kuma shiga gidan Miriam suka kashe ta a cikin gidanta a ranar 10 ga watan Mayu, shekarar 2017.

Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

'Yarta ta ɓace a shekara ta 2012. A kuma shekarar 2014 ne ta tsinci gawar 'yarta. Daga nan ta kafa ƙungiyar Colectivo de Desaparecidos de San Fernando. Waɗanda ake zargi da kisan ta sun tsere daga kurkuku.[1]

Miriam Elizabeth Rodriguez Martinez ta zauna a gundumar San Fernando a ƙasar Mexico. An kashe ta ne a ranar 10 ga watan Mayu, shekarar 2017, ranar da Mexico ke bikin Ranar Mata. Anji mata rauni sosai daga bisani kuma ta mutu a gadon asibiti.[2]

Garin San Fernando na cikin Tamaulipas, ɗaya daga cikin yankuna da ke fama da rikici a Mexico. Dangane da bayanai daga gwamnati, yankin nada mafi yawan adadin mutanen da suka bacewa a kasar.

Farmaki[gyara sashe | gyara masomin]

'Yar Maryamu, Karen Alejandra Salinas Rodriguez, ta ɓace tun a shekarar 2012. Amma Mahaifiyarta Miriam ta ci gaba da nemanta kusan shekara biyu, har zuwa shekara ta 2014 lokacin da aka sami gawar 'yarta a cikin kabarin wani da ba a sani ba. Bayan hakan, ta faɗa wa hukumomi game da kisan ‘yarta. Wasu daga cikin mutanen da aka kama da laifin kisan ‘yarta sun tsere daga kurkuku bayan an kama su. Miriam Rodriguez ta ce a cikin tambayoyin da akayi mata, ta ce ta sami barazanar kisa daga kungiyoyin masu laifi daban daban amma hukumomin yankin ba su ɗauki matakin kare ta ba. Bayan bayyanar 'yarta, tana yin ƙoƙari don taimakawa wasu iyayen waɗanda' ya'yansu suka ɓace, kuma ta kafa ƙungiyar Colectivo de Desaparecidos.[3][1] In solidarity with her, protesters raised their voices in protest the day she was killed, calling on the Mexican and U.S. governments to ensure the safety of human rights defenders.[4]

A ranar 10 ga watan Mayu, shekarar 2017, wasu gungun ‘yan bindiga suka shiga gidan Mariam suka kashe ta.

A cikin hadin kai tare da masu zanga-zanga sun daga muryar nuna adawarsu akan kisan gilla da akayi wa Miriam Elizabeth Rodriguez Martinez a ranar 10 ga watan Mayu shekarar 2017, suna kiran gwamnatocin Mexico, Amurka da gwamnatin tarayya da ke neman kare lafiyar masu kare hakkin ɗan adam su binciko waɗanda suka kashe ta kuma a hukunta su.[5]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 Villegas, Paulina (12 May 2017). "Gunmen Kill Mexican Activist for Parents of Missing Children". The New York Times (in Turanci). ISSN 0362-4331. Retrieved 2020-03-08.
  2. "Obituary: Miriam Rodríguez Martínez died on May 10th". The Economist. 20 May 2017. ISSN 0013-0613. Retrieved 13 December 2020.
  3. Agren, David (12 May 2017). "Mexican woman who uncovered cartel murder of daughter shot dead". The Guardian. Retrieved 9 March 2020.
  4. "Justice for Miriam Rodriguez" (in Turanci). Retrieved 9 March 2020.
  5. Ahmed, Azam (2020-12-13). "She Stalked Her Daughter's Killers Across Mexico, One by One". The New York Times (in Turanci). ISSN 0362-4331. Retrieved 2021-01-04.