Jump to content

Miyar Eru

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Miyar Eru

Eru kayan lambu ne daga Kamaru. Abu ne mafi soyuwa ga mutanen Bayangi,[1] na yankin Manyu a kudu maso yammacin Kamaru. Miyar ganye ne wanda ya ƙunshi ganyen da aka yanka da kyau na Eru ko okok. Ana dafa eru tare da waterleaf ko alayyaho, manja, crayfish, ko kifi busasshe, fatar saniya (kanda) ko nama.

Ana cin wannan miyar ne tare da fufu (tuwon rogo jiƙaƙƙe) ko garri.

Girke-girke Eru

  • Abincin Kamaru
  • Jerin abincin Afirka
  • Jerin kayan lambu
  1. https://cookingwithclaudy.com/tasty-eru-recipe/