Mogadishu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Somaliya.

Mogadishu (da Somaliyanci: Muqdisho; da Larabci: مقديشو )birni ne, da ke a yankin Banaadir, a ƙasar Somaliya. Shi ne babban birnin ƙasar Somaliya kuma da babban birnin yankin Banaadir. Mogadishu tana da yawan jama'a 2,425,000, bisa ga jimillar 2017. An gina birnin Mogadishu kafin karni na tara bayan haifuwan annabi Issa.