Jump to content

Mohamed Abdoulahi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mohamed Abdoulahi
Member of the National Assembly of Niger (en) Fassara

Rayuwa
ƙasa Nijar
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa National Movement for the Development of Society (en) Fassara

Mohamed Abdoulahi ɗan siyasar Nijar ne wanda ya yi aiki a gwamnatin Nijar a matsayin Ministan Ma’adanai da Makamashi daga shekarar 2004 zuwa shekarar 2010, a zamanin Shugaba Mamadou Tandja .

Harkar siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Abdoulahi ya kasance shugaban ƙungiyar Union for Democracy and Social Progress (UDPS-Amana) daga shekarar 1992 [1] [2] to 1996. Sannan ya shiga Kwamitin Tallafawa Ibrahim Maïnassara Baré (COSIMBA) da jam’iyya mai mulki ta Maïnassara, Rally for Democracy and Progress (RDP-Jama’a). Daga baya kuma, bayan kisan Maïnassara, Abdoulahi ya zama Mashawarcin Firaminista Hama Amadou kuma ya shiga Jam’iyyar National Movement for the Development of Society (MNSD) mai mulki a shekarar 2004; a zaben majalisar dokoki na watan Disamba shekara ta 2004, an zaɓe shi ga Majalisar Dokoki ta ƙasa a matsayin dan takarar MNSD.

Abdoulahi ya yi aiki na gajeren lokaci ne kawai a Majalisar Dokoki kafin a naɗa shi a cikin gwamnatin a matsayin Ministan Ma'adinai da Makamashi a ranar 30 ga watan Disambar shekarar 2004. Ya cigaba da kuma kasancewa a wannan matsayin a cikin gwamnatin da aka kafa a ranar 9 ga watan Yuni shekarar 2007 a ƙarƙashin Firayim Minista Seyni Oumarou . [3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Gouvernement du 1er mars 2007 : Iniquité et part du lion du MNSD", Roue de l'Histoire, number 342, 7 March 2007 (in French).
  2. History of the UDPS-Amana[permanent dead link] (in French).
  3. "Niger : President Mamadou Tandja approves new govt."[dead link], African Press Agency, 9 June 2007.