Mohammed Usman (General)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mohammed Usman (General)
Rayuwa
Sana'a

Manjo Janar Mohammed Takuti Usman hafsan sojan Najeriya ne, wanda shi ne Kwamandan runduna ta 81 ta sojojin Najeriya .[1]

Ya kasance Kwamandan Rundunar Sojojin Najeriya daga Shekara ta 2019 zuwa shekara ta 2023, wanda shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa a ranar 4 ga watan Agustan shekara ta 2019 domin maye gurbin kwamandan mai barin gado Birgediya Janar Umar Tama Musa.[2][3]

Usman ya taɓa rike mukamin kwamandan Guards Brigade kuma Adjutant Commanding Officer na bataliya ta 177, ya rike shugaban ma’aikata a Brigade na kwamandoji uku a matsayin Kanar na tsawon shekaru huɗu.

Ya kasance Shugaban Hulɗa da Sojoji a Hedikwatar Sojoji da ke Abuja kafin ya zama Kwamanda na 36 na Brigade na Guards.[4]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Odunsi, Wale (2019-08-04). "Nigerian Army changes Commander of Buhari's guards". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2020-10-16.
  2. "Brig-Gen Mohammed Takuti Usman takes over from Brig-Gen Umar Tama Musa as New Guards Brigade Commander". Security King Nigeria (in Turanci). 2019-08-05. Archived from the original on 2020-10-18. Retrieved 2020-10-16.
  3. "JUST IN:New Guards Brigade Commander takes over". The Sun Nigeria (in Turanci). 2019-08-05. Retrieved 2020-10-16.
  4. "Gen. Mohammed takes over as 36th GOC of Army 1 Division". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2020-04-10. Retrieved 2020-10-16.