Jump to content

Mojisolaoluwa Alli Macaulay

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mojisolaoluwa Alli Macaulay
Rayuwa
Haihuwa Surulere, 10 Oktoba 1977 (47 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Milton Keynes (en) Fassara 2003) diploma (en) Fassara
Jami'ar, Jihar Lagos Bachelor of Arts (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

MojisolaOluwa Kehinde Alli – Macaulay (née Alli) (an haife ta a ranar 10 ga watan Oktoban, 1977[1]) 'yar siyasan Najeriya ce,[2] 'yar majalisa[3][4][5][6] kuma 'yar jam’iyyar All Progressive Congress APC. Ta kasance 'yar majalisar dokokin jihar Legas, mai wakiltar mazabar Amuwo Odofin I[7] kuma shugabar kwamitin majalisar dokokin jihar Legas mai kula da harkokin mata, rage talauci da samar da ayyukan yi.[8]

Mojisolaoluwa Alli Macaulay

An haifi Mojisolaoluwa a garin Surulere, jihar Legas kuma ta fito daga tsibirin Legas-Island da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Ta yi karatun ta na firamare a Subola Nursery & Primary School 1982-1984 kuma ta kammala a Festac Primary School 1984-1990. Nan da nan ta fara karatun sakandare a makarantar sakandare ta 'yan mata ta Festac 1990-1993[9][10] kuma ta kammala a Makarantar Sakandare ta Navy Town a tsakanin shekarun 1993-1995[11] inda ta sami takardar shaidar Makarantun Yammacin Afirka (WAEC).

Ta ci gaba da karatun ta na Diploma a Open University Milton Keynes, United Kingdom[12][13] a cikin ilimin zamantakewa (2003).[11] A shekarar 2015 ta kammala Digiri dinta na farko a fannin tarihi da huldar kasa da kasa[14] daga Jami’ar Jihar Legas.[1] A 2021 kuma ta sami digiri a LAW a Jami'ar Jihar Lagos.

Rayuwa ta sirri

[gyara sashe | gyara masomin]

Ta auri Honourable Jonathan Macaulay kuma suna da yara biyu.[15]

Mojisolaoluwa ta fara aikinta akan jarida da yada labarai a shekarar 1997 a matsayin mai bayar da sanarwar Duty na Rediyon Lagos/Eko FM (1997-1999) [1], nan take ta yi aiki a matsayin mai gabatar da labarai a MITV/STAR FM na tsawon shekaru uku. 1999-2001), sannan ta koma NTA 2 Channel 5 a matsayin Mai Binciken Labarai, Mai gabatar da Labarai sannan kuma mai gabatarwa (2001-2002).

Aikin siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Ta tsaya takarar kansila a WARD B1, Amuwo Odofin a karkashin jam'iyyar Action Congress of Nigeria kuma ta yi nasara a shekarun (2010 -2013) [2] . Ta kuma kasance tsohuwar mataimakiyar shugaba, Amuwo Odofin na majalisar dokoki, karamar hukumar Amuwo Odofin.[16]

A cikin shekara ta 2019 ta fito takarar kuma ta yi Nasarar zaman 'yar majalisa a Mazabar Amuwo Odofin 1. A halin yanzu ita mamba ce a majalisar dokoki ta 9, majalisar dokokin jihar Legas.[17]

  1. 1.0 1.1 "Who be Mojisola Alli-Macaulay? wey say "Nigerian youths dey high on drugs all di time"". BBC News Pidgin. Retrieved May 12, 2021.
  2. "MOJISOLA ALLI-MACAULAY: Newbies in politics should not aim for high positions". Latest Nigeria News, Nigerian Newspapers, Politics. March 1, 2020. Retrieved May 12, 2021.
  3. "HON. MOJISOLA KEHINDE ALLI-MACAULAY – Lagos State House of Assembly" (in Turanci). Archived from the original on May 12, 2021. Retrieved May 12, 2021.
  4. "My drug comment about hoodlums, not youths — Lagos lawmaker". Punch Newspapers (in Turanci). April 16, 2021. Retrieved May 12, 2021.
  5. "EMPOWERMENT: Lagos lawmaker urges youths to support govt". Vanguard News (in Turanci). April 10, 2021. Retrieved May 12, 2021.
  6. "HON. MOJISOLA KEHINDE ALLI-MACAULAY – Lagos State House of Assembly" (in Turanci). Archived from the original on May 12, 2021. Retrieved May 12, 2021.
  7. "Constituencies – Lagos State House of Assembly". Retrieved May 12, 2021.
  8. "Admin. "More space for women equals a better Africa – Hon. Mojisolaoluwa Alli-Macaulay | National Daily Newspaper". Retrieved May 12, 2021.
  9. "'Amuwo Odofin constituency 'll benefit from my stewardship'". Latest Nigeria News, Nigerian Newspapers, Politics. February 24, 2019. Retrieved May 12, 2021.
  10. "HON. MOJISOLA KEHINDE ALLI-MACAULAY – Lagos State House of Assembly". Retrieved May 12, 2021.
  11. 11.0 11.1 "Who be Mojisola Alli-Macaulay? wey say "Nigerian youths dey high on drugs all di time"". BBC News Pidgin. Retrieved May 12, 2021.
  12. "Who be Mojisola Alli-Macaulay? wey say "Nigerian youths dey high on drugs all di time"". BBC News Pidgin. Retrieved May 12, 2021.
  13. HON. MOJISOLA KEHINDE ALLI-MACAULAY – Lagos State House of Assembly". Retrieved May 12, 2021.
  14. "HON. MOJISOLA KEHINDE ALLI-MACAULAY – Lagos State House of Assembly". Retrieved May 12, 2021.
  15. "HON. MOJISOLA KEHINDE ALLI-MACAULAY – Lagos State House of Assembly". Retrieved May 12, 2021.
  16. 'Amuwo Odofin constituency 'll benefit from my stewardship'". Latest Nigeria News, Nigerian Newspapers, Politics. February 24, 2019. Retrieved May 12, 2021.
  17. "Members – Lagos State House of Assembly". Retrieved July 12, 2021.