Jump to content

Monireh Gorji

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Monireh Gorji
Rayuwa
Haihuwa Tehran, 1930 (93/94 shekaru)
ƙasa Iran
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa Islamic Republican Party (en) Fassara
monireh gorji

Monireh Gorji malama ce a kasar iran kuma yar gwagwarmaya. ita kadai ce mace ta farko da aka fara zaba cikin kwararrun mutane guda 73 da zasu yi aiki akan kundin tsarin mulki na kasa a shekarar alif 1979. Su wannan kwararru su ke da alhakin zabe da kuma sa ido ga dukkan yadda shugaban kasa ke gudanar da ayyuka.[1]

Ayyuka da gudunmuwar data bayar

[gyara sashe | gyara masomin]

Akwai rubuce rubuce daban daban daga masana akan ayyukan Gorji da gudunmuwar ta, misali a shekarar 1980 an ambaci aiyukan ta a mukala mai suna "Mata a tsarin mulkin musulunci na Iran". Sannan ta bada gudunmuwa wajen yada kare hakki da yancin mata a kasar Iran, inda ta kafa hujja da muhimmancin kare hakkin mata da kuma rawar da mata suke takawa daga mahangar littafin Al Kur'ani mai tsarki.[2]

  1. Ervand Abrahamian (1989), "To The Masses", Radical Islam: the Iranian Mojahedin, Society and culture in the modern Middle East, vol. 3, I.B.Tauris, p. 195, Table 6, ISBN 9781850430773
  2. https://doi.org/10.1080%2F00210862.2012.726846