Moussa Seybou Kassey

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Moussa Seybou Kassey
Rayuwa
Haihuwa Dosso, 1959
ƙasa Nijar
Mutuwa 27 ga Afirilu, 2020
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, Mai tattala arziki da financial planner (en) Fassara

Moussa Seybou Kassey (1959 - 27 Afrilun shekarar 2020) ɗan siyasar Nijar ne wanda ya yi minista a ma'aikatan gwamnati da ƙwadago.[1] Ya kasance mai magana da yawun gwamnati a ƙarƙashin Firayim Minista Hama Amadou daga 17 ga Satumban shekarar 2001 zuwa 30 ga Disamban shekarar 2004.

Tarihin Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Kassey yayi karatu a matsayin masanin tattalin arziƙi, kuma ya buga littafin La politique de planification urbaine au Niger. : le cas de Niamey.[2] Ya kasance shugaban ƙungiyar Mouvement Patriotique pour la Solidarité et le Progrès, jam'iyyar siyasa a Nijar.

Daga shekarar 2014 har zuwa rasuwarsa a shekarar 2020, ya kasance Darakta Janar na Hukumar Caisse Autonome des Retraites du Niger, wata hukuma mai cin gashin kanta da ke kula da harkokin kuɗaɗen fansho na sojojin Nijar.[3]

Mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Kassey ya mutu ranar 27 ga Afrilun shekarar 2020.[4]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]