Dosso (birni)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Dosso
N1 Dosso.jpg
municipality of Niger
ƙasaNijar Gyara
babban birninDosso (sashe), Yankin Dosso, Dosso Kingdom Gyara
located in the administrative territorial entityDosso (sashe) Gyara
coordinate location13°3′0″N 3°12′0″E Gyara
located in time zoneUTC+01:00 Gyara

Dosso birni ne dake kan kwanar kudu maso yammacin kasar Nijar. Birnin na tsakanin kilomita 130 - 140 (mil 81-87) kudu maso gabashin babban birnin kasar wato Niamey a kan marabar hanyar zuwa birnin Zinder kasar Benin. Birni na bakwai mafi yawan jama'a a kasar ta Nijar kuma mafi girma a yankin gundumar Dosso, a kidayar shekarar 2001 akwai mutane kimanin 43,561. Birnin ne cibiyar gundumar wanda ya kunshi bangarorin gudanarwa guda biyar dake kudu maso yammacun kadar Nijar.

Tarihi[gyara sashe | Gyara masomin]

Masrautar Dosso na zaunene a garin na Dosso, Kafin shigowar turawan mulkin mallaka masarautar Zarma ce ta mamaye dukkan yankunan na Zarma. Sarkin gargajiyar yankin ana kiran sa da Zarmakoy ko Djermakoy na Dosso. Ma'ana Sarkin Zarma ko (Djerma).

Muhallai[gyara sashe | Gyara masomin]

Manyan muhallan birnun akwai Masarautar Djermakoy da gidan ajiye kayan tarihi wanda yake daga cikin guwaren abubuwan mamaku na Majalisar dinkin duniya wato UNESCO World Heritage Sites a 2006.

Sufuri[gyara sashe | Gyara masomin]

Birnin na Dosso mahadar kasuwanci ne na shiga da fitar kaya daga birnin Kwatano na kasar Benin. Sakamakon shigo da kaya zuwa birnin Niamey ne Dosso ta zama matattarar sufuri na kanana da manyan motoci. Akwai hanyar jirgin kasa dake kan aiki a halin yanzu.

A wani kari kuma akwai shirin gina tashar sauke kaya ta doron kasa.

Sanannun mazauna birnin[gyara sashe | Gyara masomin]

  • Rabiou Guero Gao - Dan wasan tsere na dogon zango a kasar Nijar.
  • Zakari Gourouza - Dan wasan Olympic na kasar Nijar