Muhammad Mustapha Abdallah
Muhammad Mustapha Abdallah | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Hong (Nijeriya), 13 Nuwamba, 1954 (70 shekaru) |
Karatu | |
Makaranta |
Sam Houston State University (en) Jami'ar Ahmadu Bello Jami'ar Tsaron Nijeriya |
Sana'a |
Muhammad Mustapha Abdallah (An haifeshi ranar 13 ga watan Nuwamban shekarar 1954) a Hong, jihar Adamawa shi lauya ne kuma masani akan harkokin tsaro na Najeriya. Ya kasance tsohon shugaban jami'in Hukumar Yaki da Sha da Muggan Kwayoyi ta Najeriya (NDLEA).
Karatu
[gyara sashe | gyara masomin]A shekarar 1977, Mohammad Abdallah ya samu takardar shedar karatu a makarantar horas da sojoji ta Najeriya (NDA). A 1988, Ya sami digiri a fannin Siyasa da daga Jami'ar Sam Houston State University, Huntville, Texas, ta kasar Amurka.[1] Ya kuma yi digirin digirgir a fannin harkokin gwamnati.
A shekarar 2005, ya kuma samu digirin digirgir a fannin shari’a a jami’ar Ahmadu Bello Zariya da kuma digirin farko a fannin shari’a a makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya a shekarar 2006.[2] A shekarar 2011, Mohammad Abdallah ya samu digiri na biyu a fannin shari’a daga Jami’ar Ahmadu Bello Zariya.
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Mohammad Abdallah ya yi aikin sojan Najeriya na tsawon shekaru 30. Ya yi ritaya a matsayin Laftanar Kanar. A watan Janairun 2016, Shugaba Buhari ya naɗa Mohammad Abdallah a matsayin shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA. Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir David Lawan ne ya sanar da nadin nasa ranar Litinin, 18 ga Janairun shekarar 2016.
A watan Janairun 2021, an kori Mohammad Abdallah a matsayin Shugaban NDLEA.
A cewar wasikar da sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya aikewa Abdullah, an umurci Abdullah ya mika ayyukan hukumar ga Mista Shadrach Haruna a ko kafin ranar 10 ga watan Junairun shekarar 2021.[3] Abdullah yayi yunkurin fara daukar ma'aikata masu yawa, sa'o'i 24 kadan bayan ya samu wasikar mika mulki. Sai dai shugaba Buhari ya dakatar da daukar aikin.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://www.vanguardngr.com/2016/01/fg-appoints-muhammad-abdallah-as-new-ndlea-chairman/
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-03-26. Retrieved 2022-03-26.
- ↑ https://thenationonlineng.net/abdallah-is-new-chair-of-ndlea/