Muhammadu Gwarzo
Appearance
Muhammadu Gwarzo | |
---|---|
Rayuwa | |
Karatu | |
Harsuna | Hausa |
Sana'a | |
Sana'a | marubuci |
Muhammadu Gwarzo Yana daya daga cikin marubuta na farko na Kasar Hausa. Inda ya rubuta littafinsa mai suna ‘Idon Matambayi’. Ba kamar yadda su Abubakar Imam da su Bello Kagara suka rubuta littattafan su ba. Shi Muhammadu Gwarzo ya bada labarin mugayen mutane ne da rayuwarsu da yanda suke karewa a rayuwarsu.[1]
Wallafa
[gyara sashe | gyara masomin]- Idon Matambayi
Idon Matambayi yazo da wani sabon salo ne a wannan lokacin inda ya bada labarin wani tawaye na barayi ba kamar yadda aka saba ba na jin labaran mutanen kirki. A cikin Idon Matambayi yazo ne da labaran barayi da karshen su da kuma hukuncin da suka fuskanta a rayuwarsu. Duk da cewa littafin bai samu daukaka ba kamar su Magana Jari Ce, da su Ruwan Bagaja amma littafin ya ilmantar.[1]
Bibiliyo
[gyara sashe | gyara masomin]- Furniss, Graham. (1996). Poetry, prose and popular culture in Hausa. International African Institute. Edinburgh: Edinburgh University Press for the International African Institute. ISBN 978-1-4744-6829-9. OCLC 648578425.