Jump to content

Muhibbat Abdussalam

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Muhibbat Abdussalam tsohuwar jaruma ce a masana'antar fim ta Hausa wato kanniwud tayi tashe a masana'antar anfi sanin ta da suna Rabi Yar Caburos saboda Wani fim nata da tayi ta fito a sunan.[1]

Muhibbat Abdussalam shine Cikakken sunan ta jaruma ce a masana'antar film ta Hausa wato masana'antar Kannywood, ta Dade a masana'antar fim tayi tashe a masana'antar tayi fina finai da dama a cikin masana'antar, ita kadaice darakta mace a masana'antar fim ta fara da zama jaruma daga baya ta zama darakta da taimakon mijinta. Tayi aure shekaru goma Sha biyar kenan inda kuma ta auri darakta Hassan Giggs na masana'antar tana da Yara guda uku mata dashi. Ta shigo masana'antar fim ta Hausa a shekarar 2000 ta fara da zama jaruma daga Nan ta fara soyayyah da darakta Hassan Giggs inda sukai aure bayan sunyi aure ne mijinta ya jagorance ta ta zama darakta.[2] Bayan harkan fim tana sana,a na gyaran jiki na mata.[3]

  1. https://hausa.legit.ng/1150990-dandalin-kannywood-kun-ji-abun-da-aka-yi-wa-tsohuwar-jaruma-muhibbat-abdussalam.html
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-30. Retrieved 2023-07-30.
  3. https://www.premiumtimesng.com/entertainment/156044-meet-kannywoods-only-female-director-muhibbat-abdussalam.html