Muhimmancin Azumi ga lafiyar dan Adam
Gabatarwa
[gyara sashe | gyara masomin]Al’ummar musulmai a duk fadin duniya sukan dauki Azumi a lokacin daya (Ba tare da sunci abinci ba ko ruwa) tun daga fitowar Alfijir har zuwa faduwar rana a cikin watan RAMADAN.[1] Duk da cewa, ba ana yin azumi ne domin samun lafiya ba, Azumi Umurnine na Allah (S.W.A), Amma tare da haka Kimiyar Zamani ta tabbatarda Azumin (Musamman na watan Ramadan), Yana taka muhimmiyar Rawa wajen Samun Lafiya (Wannan shine bayanin da zanyi). Shi dai Azumi na wajaba ne a kan mutum mai cikakkiyar lafiya, ta hankali da ta jiki, ba mai raunin lafiya ko yaro ba. Wannan shi ya sa a addinance da kuma a likitance ba kowa ne aka yarda ya yi azumi ba. Duk da haka kuma, akwai marasa lafiyar da azumi kan yi wa amfani sosai wadanda su ma zan yi dan bayanin amfanin Azumi a gare su.
Ilimin likitanci ya tabbatar da cewa yin Azimi yana daga mafi muhimmancin hanyar da mutum zai samu lafiya, kuma abu ne na tilas a rayuwar mutum ga wanda yake son lafiyarsa ta inganta [2]. Hikimar Allah madaukaki ta tabbatar da cewa hatta dabbobi suna barin cin abinci na wasu kwanaki a shekara don samun daidaito a rayuwarsu da lafiyar jikinsu, masu dabbobin sukan dauke shi wani lokaci a matsayin rashin lafiya alhalin lafiyar dabbobinsu qalau. Bincike ya nuna cewa kowace dabba tana da wani lokaci da dole ne ta takaita cin abinci a cikinta don samun daidaito a lafiyar jikinta.[3]
Azumi da Lafiyan Dan Adam
[gyara sashe | gyara masomin]Babu Shakkah cin abinci bada yawa ba yana sanya hutun hanji da yake takura ciki da sanya yawan maiko da kiba su taso su kange kirji ta yadda huhu zai kasa numfasawa cikin annashuwa, don haka ne ma mutane da yawa suka samu dama a lokacin Azumi don su dawo da kansu daidai da tsara cikinsu da rage kibarsu don samun sa’ida da walwalar jiki. Akwai bayanai masu yawa na likitanci da suke nuna karantuwar gubar da take a cikin abinci da fitar ta daga jikin mutum sakamakon yin Azumi, Na tattara bayanai masu yawa kan wannan lamarin, sai dai ba ni da lokacin da zan iya kawo su cikin wannan gajeren bayani, amma ina fatan dan kadandin zai wadatar matukar za a iya yin aiki da shi. Azumi yana taimakawa wurin kona sukari, da mai da yake cikin hanta da jini da fata, don samun lafiyar zuciya. Akwai bayanai masu yawa da likitoci irin su; Mark Pardon, Cases Karyl, Micheal Angilo, Dakta Muhammad Sa’id Suyuti, Dakta Muhammad Arrawi, da sauran manyan likitocin duniya suka yi kan wannan lamarin da yake nuna matukar mahimmanci da wajabcin Azumi ga rayuwar mutum[4]. Mutumin da yake jahiltar sirrin jikinsa sai ya dauka yunwa zata illa ta shi ne sakamakon yin Azumi, alhalin yana da ajiyayyen sukari da yake samun amfanin jiki a matsayin gulokojin da aka ajiye a hantarsa wanda zai iya amfana daga gare shi tsawon lokaci, sannan sai ya karkata ga ajiyayyun mai da yake jikinsa, wannan shi ne sirrin da ya sanya zamu ga mutum yana iya amfani da ruwa har kwanaki 40. Sai kuma jiki ya koma tara wasu sinadirai sakamakon hakan ya sake amfani da su don gina gabobinsa da daidaita tsarin rayuwarsu a lokacin Azumi[5]. Sai dai duk da muhimmancin Azumi ba a yarda kuma a wuce gona da iri wurin yunwata kai ba, don haka daidaito shi ne abin nema (Ba’ason yin Tsallen Badake)[6]. A shekarar 1964 Dreanik da masu taimaka masa sun kawo bayanai masu hadari ga jiki idan ya ci gaba da yunwatuwa tsawon lokaci da ya wuce kwanki 30–40. A nan ne zamu ga hikimar shari’ar musulunci da ta yarda mutum ya yi azumi 30 ne kawai. Lallai tafarkin Addinin Manzon Allah (Saww) ne kawai ya yi daidai da ilimi a wannan fagen kamar yadda zamu iya gani.
Amfanin Azumi ga Lafiyan Dan Adam
[gyara sashe | gyara masomin]Shin ko wane irin tasiri azumi ke yi a jikin mutum? Dr Lawal Musa Tahir wani kwararren likita da ke asibitin Nizamiye a birnin Abuja, ya lissafa alfanun azumi ga jikin dan adam guda takwas[7]: 1. Rage yawan sikari daga jikin dan adam 2. Kona kitse 3. Rage teba 4. Inganta lafiyar zuciya 5. Inganta garkuwar jiki 6. Tsaftace jiki da hutar da sassan jiki 7. Inganta lafiyar kwalkwalwa 8. Hana kasala 9. Bayanan bidiyo, 10. Maraba da Watan Ramadan Rage yawan sukari daga jikin dan adam A ka'ida dai jikin mutum ba ya shiga yanayin azumi sosai sai an shafe sa'a takwas bayan abinci na karshe da mutum ya ci. Wannan shi ne lokacin da cikin mutum ya gama narkar da abubuwan gina jiki da ya samu daga abincin. Jim kadan bayan wannan lokacin, jikinmu zai koma wa sikarin da ke adane a hanta da tsokar jikinmu domin samun karfi. Bayan dan lokaci kadan, idan sikarin ya kare, to kitse ne zai koma wuri na gaba da jiki zai iya samun karfi daga gare shi.[8]
Kone kitsen jikin dan adam
[gyara sashe | gyara masomin]Idan jikin mutum ya fara kone kitse, wannan na taimakawa wajen rage kiba da rage maiko da kuma rage yiwuwar mutum ya kamu da ciwon siga.
Rage teba
[gyara sashe | gyara masomin]Sakamakon kone sukari da kitse a jikin dan adam, hakan na sa nauyi da kibar dan adam ta ragu wadda hakan ce manufar motsa jiki.
Inganta lafiyar zuciya
[gyara sashe | gyara masomin]Masana na cewa mutane da dama kimanin kaso 31.5 da ke mutuwa na mutuwa ne sakamakon cututtuka masu alaka da ciwon zuciya. Dr Tahir ya ce azumi na inganta lafiyar zuciya kasancewar yana kone kitse sannan ya kawar da teba, al'amarin da ke daidaita sauka da hawan jini.
Inganta garkuwar jiki
[gyara sashe | gyara masomin]Da zarar an kone sukari da kitse kuma an rage teba sannan an samu lafiyar zuciya to dan adam ya kan samu garkuwa da kuzari fiye da lokacin da ba ya azumi.[9] Ita kuma garkuwa na taimaka wa jiki ne wajen hana kamuwa da wata cuta ko kuma cutar ba za ta yi tasiri a jikin dan adam ba.
Tsaftace jiki da hutar da sassan jiki
[gyara sashe | gyara masomin]Idan aka ci rabin watan Ramadan, jikin mutum yana sabawa da azumi. Hanji da koda da huhu da ma fatar mutum na tsaftace kansu. Sannan sassan jikin da ke aikin tace abinci lokacin da mutum ya ci abincin za su huta ne lokacin azumi.
Inganta Lafiyar kwakwalwa
[gyara sashe | gyara masomin]Kamar yadda motsa jiki yake sanya kwakwalwa ta yi aiki yadda ya kamata, to sakamakon azumi ana iya samun wannan alfanu.
Hana kasala
[gyara sashe | gyara masomin]Idan mutum ya ci abinci sannan ya sha ruwa abin da ke biyo baya a mafi yawan lokaci shi ne kasala. To amma a lokacin azumi babu irin wannan kasala kasancewar ba a ci abinci ba.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://hausa.legit.ng/1325799-ramadan-amfanin-azumi-ga-lafiyar-dan-adam.html
- ↑ https://hausa.legit.ng/1325799-ramadan-amfanin-azumi-ga-lafiyar-dan-adam.html
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-26. Retrieved 2023-03-26.
- ↑ https://hausa.legit.ng/1325799-ramadan-amfanin-azumi-ga-lafiyar-dan-adam.html
- ↑ https://hausa.legit.ng/1325799-ramadan-amfanin-azumi-ga-lafiyar-dan-adam.html
- ↑ https://hausa.legit.ng/1325799-ramadan-amfanin-azumi-ga-lafiyar-dan-adam.html
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-26. Retrieved 2023-03-26.
- ↑ Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Azumi?
- ↑ https://hausa.legit.ng/1325799-ramadan-amfanin-azumi-ga-lafiyar-dan-adam.html