Muri
Muri | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | Jahar Taraba | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Muri, Gari ne wanda yake da masarautar gargajiya a Jalingo kuma tana da sarautar lamba ɗaya wato (Emir) garin ya mamaye karamar hukumar Karim Lamido ARDO KOLA Yoro, Karamar Hukumar Taraba da sauran su, garin yana Arewa maso yammacin jihar Taraba a gabashin Najeriya, kimanin tsakanin 9° da 11° 40′ E. da 7° 10′ da 9° 40′ N.Kogin Benuwai na kusa da garin miuri yankin kudancin kogin shi yake shayar da kogunan da suka fito daga yankin Kamaru zuwa Binuwai. A cikin shekara ta 1991, an kuma kiyasta garin yana da yawan jama'a 56,570. Sai dai kwarin Benuwai yana da yanayin da turawa basa iya zama ba a garin, sai dai kuma akwai wurare a arewacin lardin, kamar ƙauyen Fula na Wase a kudancin tsaunukan Murchison, wanda wannan kuma wurin yana bada yanayi mai kyau.[1][2] An fi amfani da harsunan Tula–Waja irin su Dadiya da Bangwinji ana magana da su gefen tsaunukan Muri.
Tarihin Muri
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin shekara ta 1817, aka kafa garin Muri a matsayin wanda Fulani ne suka kafa shi bayan jihadinsu.[3] Daga shekarar 1892 zuwa 1893 ƙasar Faransa tazo garin da sunan kariyar ta gaskiya, ƙarƙashin Gwamna Louis Mizon (b. 1853 - d. 1899). A cikin shekara ta 1901 garin yanda faɗi kusan 25,800 m². lardin da ke ƙarƙashin mulkin Birtaniya na Arewacin Najeriya, mai iyaka daga kudu (a) sai daga Kudancin Najeriya, kudu maso gabas (SE) sai ta gabas (E) tayi iyaka da yankin Kamaru wanda Jamus ta mulka. Sai Arewa (N) ta lardin Yola.[1] Sai ta yamma (W) tayi iyaka da Bauchi. Sai yamma kuma tayi iyaka da wani yankin Nasarawa da Bassa mai kimanin mutane 828,000. Ƙaramar masarautar Katsena-Allah ta kai kudu da Benuwai sosai yamma da 9° E., gwargwadon iyakar sauran lardin. Lardin yana da arzikin dazuzzuka, kuma Kamfanin Neja yana kula da tashoshin kasuwanci a gaɓar kogin. Ana noman auduga, saƙa da rini sauran su wannan yaba mutane damar samun aiki ga dubban mutane. Haka Lardin Muri ya haɗa da tsohuwar daular Jukun tare da ƙananan garuruwan Fulani daban-daban da kuma wasu ƙabilun maguzawa, waɗanda a cikinsu akwai ‘yan ƙabilar Munshi waɗanda suka mamaye lardunan Nassarawa da Bassa, na cikin waɗanda suka fi fama da tashin hankali. Yan ƙabilar Munshi sun mamaye kusan m² 4000, a gundumar Katsena-Alah. Ƙabilun maguzawa a arewacin lardin sun kasance suna cin naman mutane, marasa bin doka da oda, waɗanda suka daɗe suna nuna fushinsu da kashe-kashenn ’yan kasuwa masu fatauci zuwa Bauchi suna cikin haɗari, kuma sun daƙushe kasuwannin kwarin Binuwai (Benue valley) da Kamaru daga jihohin Hausa duk Hanyoyin da suka san ana bi sai da suka tare ta, daman hanyoyi biyu ne kawai, ɗaya ta Wase ɗayan kuma ta Gatari. A kudancin lardin maguzawa makiya sun rufe hanyar shiga Kamaru sai ta hanyoyi biyu, Takum da Beli. Ƴan kasuwan Hausawa na lardin Muri yana masu wahala bin wannan waɗannan hanyoyin ga haɗari da kashe-kashe an sami sauƙi sune a lokacin da gwamnatin Birtaniya tazo.
Muri ya zo ne a ƙarƙashin mulkin Birtaniya a shekara ta 1900. Babban yunƙurin gwamnatin shi ne taimakawa wajen buɗe hanyoyin kasuwanci. A cikin shekara ta 1904 wani balaguro da aka yi kan masu cin naman mutane ya haifar da kame manyan sansanoninsu da matsugunai tare da buɗe kasuwannin manyan gundumomi, hanyoyin da ke zuwa Binuwai sun kasance babu matsala lami lafiya. A cikin shekara ta 1905 wani balaguron yaƙi da Munshi, wanda ya zama dole ta hanyar kai hari ba gaira ba dalili a tashar Kamfanin Neja a garin Abinsi. Rashin wata hukuma ta tsakiya ya jinkirta aiwatar da shirin mayar da lardin ƙarƙashin kulawar masu gudanarwa. An kuma tsara gwamnatin a bisa tsari irin na sauran Arewacin Najeriya, kuma a ƙarƙashin wani Bature. An raba shi zuwa sassa uku na gudanarwa - gabas, tsakiya da yamma - tare da hedkwatarsu a garin Lau, Amar da Ibi. An kafa kotunan shari'a na lardi da na asali. An kai telegraph din zuwa garin Muri. Muri na ɗaya daga cikin lardunan da cinikin bayi ya fi ƙarfi a cikinsu, kuma matsayin da yake tsakanin ƙasar Jamus da ƙasashen Hausa ya sanya ta a farkon gwamnatin Burtaniya ta zama hanyar da aka fi so wajen safarar bayi.[1]
Sarakunan Muri
[gyara sashe | gyara masomin]No. | Sunan mai mulki | Fara mulki | Ƙarshen mulki |
---|---|---|---|
1 | Hamman Ruwa dan Usman | 1817 | 1833 |
2 | Ibrahim dan Hamman Ruwa | 1833 | 1848 |
3 | Hamman dan Hamman Ruwa | 1848 | 1861 |
4 | Hamadu dan Bose | 1861 | 1869 |
5 | Burba dan Hamman | 1869 | 1873 |
6 | Abubakar dan Hamman Ruwa | 1873 | 1874 |
7 | Muhammadu Nya dan Abubakar | 1874 | 1897 |
8 | Hasan dan Muhammadu Nya | 1897 | 1903 |
9 | Muhammadu Mafinɗi dan Muhammadu Nya(Honorary Knight Commander of the Order of the British Empire, Awarded by King George V ) (b. 1868 – d. *1953)[4] | 1903 | 1953 |
10 | Muhammadu Tukur dan Muhammadu Nya | 1953 | 25 Oktoban 1965 |
11 | Umaru Abba Tukur | 6 Nuwamban 1965 | 12 Augustan 1986 (sauke shi akayi) |
12 | Alhaji Abbas Njidda Tafida | 13 Yuni 1988 | har zuwa yanzu |
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 One or more of the preceding sentences incorporates text from a publication now in the public domain: Chisholm, Hugh, ed. (1911). "Muri". Encyclopædia Britannica. 19 (11th ed.). Cambridge University Press. p. 35.
- ↑ Kleinewillinghöfer, Ulrich. 2014. The languages of the Tula – Waja Group. Adamawa Languages Project.
- ↑ Victor N. Low (1972). Three Nigerian Emirates: A Study in Oral History. Northwestern University Press. p. 100. ISBN 978-0-810-1037-19.
- ↑ "Mafindi website". Archived from the original on 2020-11-25. Retrieved 2022-02-12.
Mahaɗar link ta waje
[gyara sashe | gyara masomin]- Wikipedia articles incorporating a citation from the 1911 Encyclopaedia Britannica with Wikisource reference
- Wikipedia articles incorporating text from the 1911 Encyclopædia Britannica
- Webarchive template wayback links
- Articles without coordinates
- Sokoto Caliphate
- French West Africa
- Populated places in Taraba State
- 1817 establishments in Africa
- Pages using the Kartographer extension