Jump to content

Mykhailo Mudryk

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mykhailo Mudryk
Rayuwa
Cikakken suna Михайло Петрович Мудрик
Haihuwa Krasnohrad (en) Fassara, 5 ga Janairu, 2001 (23 shekaru)
ƙasa Ukraniya
Harshen uwa Harshan Ukraniya
Karatu
Harsuna Harshan Ukraniya
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  FC Shakhtar Donetsk (en) Fassara-
 
Muƙami ko ƙwarewa winger (en) Fassara
Tsayi 175 cm
Mudryk
Mykhailo mudryk Dan wasan kwallon kafa na kasar Ukraine

Mykhailo " Misha" Petrovych Mudryk (an haifeshi ranar 5 ga watan Janairu, 2001). Kwararren dan wasan kwallon kafa ne dan asalin kasar Ukraine wanda ke taka leda a matsayin dan wasan gaba ga kungiyar kwallon kafan Premier League ta Chelsea da tawagar kasa ta Ukraine.[1]

Mudryk ya fara aikinsa ne a makarantan koyon kwallon kafa ta Metalist Kharkiv da Dnipro , kafin ya koma kungiyar Shakhtar Donetsk a shekarar 2016.[2] Ya fara buga wasansa na farko bayan shekaru biyu da zuwansa kungiyar, sannan anbada aronshi ga Arsenal Kyiv da Desna Chernihiv.[3] A cikin 2023 ne kuma, ya koma kungiyar ta Chelsea ta kasar Ingila a cikin canja wuri mai daraja akan Yuro €70 miliyan (£ 62 miliyan), wanda ya sa ya zama dan wasan kwallon kafa na Ukraine mafi tsada a kowane lokaci kuma dan wasa mafi tsada da aka taba sayowa daga gasar Premier ta Ukraine.

Mudryk ya kasance tare da kungiyar manya ta kasa a shekarar 2022, wanda a baya yakasance ne tareda kungiyar kasa ta matasa.