Jump to content

Nassor Hamoud

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Nassor Hamoud
Rayuwa
Haihuwa Temeke District (en) Fassara, 23 ga Maris, 2001 (23 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
 

Nassor Saadun Hamoud (an haife shi ranar 23 ga watan Maris 2001), wanda aka fi sani da Nassor Hamoud, ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Tanzaniya wanda ke taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Šumadija Aranđelovac ta Serbian League West.

Aikin kulob

[gyara sashe | gyara masomin]

A kasarsa Tanzania Hamoud ya buga wasa a kulob ɗin Kagera Sugar ta gasar Premier ta Tanzaniya. [1] Daga shekarun 2018 zuwa 2020 ya buga wa Tersana SC na rukunin biyu na Masar wasa. A cikin watan Fabrairu 2020 ya yi tsalle zuwa Turai kuma ya rattaba hannu a kulob ɗin OFK Žarkovo na Gasar Farko ta Serbia na kakar 2019-20 kan kwantiragin shekaru biyu. Gabaɗaya, ya buga wasanni biyu a ƙungiyar tare da halarta na farko a ranar 30 ga watan Mayu 2020 da FK Zlatibor Čajetina. [2] Daga nan sai ya koma FK Šumadija Aranđelovac kafin a ba da shi rance ga kungiyar kwallon kafa ta MFK Vyškov a 2021.[3]

Ayyukan kasa da kasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Hamoud ya kasance cikin tawagar Tanzaniya a gasar cin kofin Afrika ta matasa ta 'yan kasa da shekaru 20 na 2021, kuma ya buga dukkan wasanni ukun da kungiyar ta buga.[4] [5]

A cikin watan Maris 2021 an sanya Hamoud a matsayin daya daga cikin 'yan wasan da ke kasashen waje a jerin 'yan wasan Kim Poulsen na wucin gadi na manyan wasannin sada zumunta biyu da Kenya. [6] A watan Mayun wannan shekarar, an sake saka shi cikin tawagar wucin gadi don wasan sada zumunci da Malawi amma bai yi jerin gwano na karshe ba.[7]

  1. "Kagera Sugar Roster" . Kagera Sugar FC. Retrieved 15 July 2021.
  2. "NINJA, NASSORO MOHAMMED WAPATA DILI LA KUKIPIGA ULAYA, WAKWEA PIPA LEO" (in Swahili). Saleh Jembe. Retrieved 15 July 2021.
  3. "Prva Liga profile" (in Serbian). Prva Liga. Retrieved 15 July 2021.
  4. Edward, Muambo. "Black Satellites To Face Ngorongoro Heroes In Group C" . sportsworld2day.com. Retrieved 15 July 2021.
  5. "Soccerway profile" . Soccerway. Retrieved 15 July 2021.
  6. "Tanzania traveling team to Kenya revealed" . pepeta.co.ke. Retrieved 15 July 2021.
  7. Omary, Majuto (28 May 2021). "Kim Poulsen names provisional Taifa Stars squad, drops 17" . The Citizen. Retrieved 15 July 2021.