Nawfia

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Nawfia

Wuri
Map
 6°10′N 7°01′E / 6.17°N 7.02°E / 6.17; 7.02
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaAnambra

Nawfia gari ne, da ke cikin ƙaramar hukumar Njikoka a jihar Anambra, a Najeriya. Nawfia na kewaye da makwabtan garuruwan da suka haɗa da; Enugwu Ukwu, Awka (Umuokpu), Nise, Amawbia da Enugwu Agidi. Ƙabilar Igbo ne suka mamaye garin, kuma ana kyautata zaton garin na ɗaya daga cikin garuruwan da suka zama mahaifar ƙabilar Igbo. Yawancin mazaunanta ƴan Gargajiya ne da Kiristoci (tare da ’yan Anglika da Roman Katolika waɗanda ke da rinjaye). Harsunan Ibo, Turanci da kuma Turancin pidgin sune manyan yarukan da ake magana da su a Nawfia.

Garin na da gundumomi guda biyu gasu kamar haka: Ifite (Ward 1) da Ezimezi (Ward 2). Garin ya kuma daidaita ƙauyuka goma da suka haɗa da: Adagbe Mmimi, Enugo Mmimi, Eziakpaka, Iridana, Urualor/Uruejimofor, Uruorji, Urukpaleri, Umuriam, Umuezunu da Umukwa.

Jagoranci[gyara sashe | gyara masomin]

Gwamnatin da ke kula da harkokin Nawfia ta ƙunshi manyan hukumomi uku da suka haɗa da Igwe na Nawfia, Shugaban ƙungiyar Nawfia Progressive Union da kuma Nze/Ozo Council.

Igwe na Nawfia shine mai kula da al'adu kuma shine mai kula da harkokin tsaro da filaye. Shugaban Janar shi ne ke kula da harkokin gudanarwa na garin (tare da shugabannin ƙauyuka na kowane ƙauye) da ayyukan majalisa. Majalisar Nze/Ozo ƙungiya ce ta dattawan ''mai suna'' wadanda ke taimakawa Igwe wajen kiyaye al'adu da al'ada da kuma magance rikice-rikice.

Sarauta[gyara sashe | gyara masomin]

Tsohon sarkin gargajiya na garin shine Mai Martaba Sarkin, Igwe Sir FFBC Nwankwo (Osuofia na Nawfia). Basaraken gargajiya na yanzu shine Mai Martaba Dr. Shadrach Moguluwa Tsohon shugaban Janar Sir Nonyelu Okoye (Eze Udo). Shugaban Nawfia Progressive Union na yanzu shine Cif Sir Nathan Enemuo (Eze Ego).

Nawfia na ɗaya daga cikin garuruwan da suka haɗa da dangin Umunri. Nawfia tare da Enugwu Ukwu, Enugwu Agidi, da Agu Ukwu, ana kyautata zaton sune inda aka samo asalin zuriyar Igbo. A cewar labarin Igbo, Nawfia (wanda ake kira Nnọfvịa a yaren gida), shi ne ɗa na biyu ga Nri kuma mafarauci a sana’a. Mahaifin Nri, Eri ana kyautata zaton shi ne uban ɗaukacin duk wani Ba-inyamure.[1]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Daily, Times (4 January 2017). "Traditional ruler of Nawfia Community in Njikoka Local Government Area of Anambra State". Daily Times. Lagos, Nigeria.