Nneka Onyeali-Ikpe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Nneka Onyeali-Ikpe (an haife ta a ranar 28 ga watan Yuli, 1964) 'yar kasuwan Najeriya ce kuma ma’aikaciyar banki. Ita ce mace ta farko a matsayin Manajan Darakta kuma babbar jami'a a bankin Fidelity Nigeria.[1] [2]

Ƙuruciya[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Nneka Onyeali-Ikpe a Awka, Jihar Anambra, a Gabashin Najeriya. Ta kuma zauna a Owerri, Jihar Imo, inda ta yi karatu a Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya.[3]

Ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

Onyeali-Ikpe tana da digiri na shari'a daga Jami'ar Najeriya, Nsukka. Hakanan tana da digiri na biyu a fannin shari'a daga King's College London.[4] [5]

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin shekarar 1990, ta fara aiki a banki a matsayin legal officer na bankin nahiyar Afirka da ya rushe a yanzu. Daga baya ta yi aiki a matsayin ma'aikaciyar ajiya a bankin First African Trust Bank. Daga baya ta koma Zenith Bank da Standard Chartered Bank bi da bi.[6][7]

Bankin Enterprise[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 2011, ta shiga bankin Enterprise a matsayin babbar darektar ayyukan bankin a Legas da sauran wurare a yankin Kudu-maso-Yamma a Najeriya. [8]

Bankin Fidelity[gyara sashe | gyara masomin]

Onyeali-Ikpe ta shiga bankin kasuwanci na Fidelity a matsayin babbar darakta a watan Janairu, 2015. Bankin Fidelity ya sanar da Onyeali-Ikpe a matsayin manajan darakta a cikin watan Disamba 2020.[9]

Rayuwa ta sirri[gyara sashe | gyara masomin]

Onyeali-Ikpe ta na da aure.[10]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Nneka Onyeali-Ikpe, Fidelity Bank PLC: Profile and Biography" . Bloomberg.com . Retrieved 2021-02-06.
  2. "Onyeali-Ikpe assumes office as MD/CEO of Fidelity Bank" . Businessday NG . 2021-01-04. Retrieved 2021-02-06.
  3. Eboigbe, Epa Ogie (2021-01-04). "MEET NNEKA ONYEALI-IKPE, THE NEW CEO OF FIDELITY BANK" . Epa. Retrieved 2021-02-06.
  4. "All eyes on first female MD of Fidelity Bank as Onyeali-Ikpe resumes" . Vanguard News . 2020-12-23. Retrieved 2021-02-07.
  5. MarketScreener. "Fidelity Bank : Appoints Onyeali-Ikpe As CEO Designate | MarketScreener" . www.marketscreener.com . Retrieved 2021-02-07.
  6. Nairametrics (2015-09-06). "Here Is What You Need To Know About Fidelity Bank's Two New Executive Director's" . Nairametrics. Retrieved 2021-02-06.
  7. Taiwo, Lukmon (2020-12-23). "Facts on Incoming First Female Fidelity Bank MD, Nneka Onyeali-Ikpe" . P.M. News . Retrieved 2021-02-06.
  8. Awojulugbe, Oluseyi (2021-01-03). "Onyeali-Ikpe assumes office as Fidelity Bank CEO" . TheCable . Retrieved 2021-02-06.
  9. "Onyeali-Ikpe assumes Office as MD/CEO of Fidelity Bank" . 2021-01-03. Retrieved 2021-02-07.
  10. 78marketing (2021-02-06). "Ken Onyeali Ikpe's wife Nneka made md-designate at Fidelity Bank" .