Jump to content

Obi Aguocha

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Obi Aguocha dan siyasan Najeriya ne kuma ɗan majalisar wakilai ta ƙasa ta 10 daga mazaɓar Ikwuano/Umuahia North/Umuahia ta kudu ta jihar Abia a bisa kan tikitin jam'iyyar Labour Party, LP. [1]

Aikin siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Aguocha na LP ya fafata ne a zaɓen ‘yan majalisar wakilai na mazaɓar Ikwuano/Umuahia ta Arewa/Umuahia ta kudu a jihar Abia a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023 da ɗan takarar jam’iyyar PDP kuma shugaban majalisar dokokin jihar Abia Chinedum Orji. [2] Orji ɗan tsohon gwamnan jihar Abia, Theodore Orji ne. Aguocha wanda ɗan siyasa ne mai kishin ƙasa kuma wanda ya taɓa tsayawa takarar gwamna ya samu kuri’u 48,199 inda ya kayar da Orji wanda ya samu kuri’u 35,195. [3] Nasarar da Aguocha ya samu kan Orji na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka tada hankalin siyasa sakamakon 'sakamakon Peter Obi' ɗan takarar shugaban ƙasa na LP. [4] [5]

  1. John-Mark, Aisha (2023-02-27). "Abia State Speaker Loses Constituency to LP Candidate". Voice of Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-04-26.
  2. Cyril (2022-08-02). "2023: Peter Obi needs his party members at NASS -LP Reps candidate". The Sun Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-04-26.
  3. Nigeria, News Agency of (2023-02-27). "Abia speaker loses Reps seat to Labour candidate". Peoples Gazette (in Turanci). Retrieved 2023-04-26.
  4. "Abia Speaker loses to Labour Party greenhorn". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2023-02-28. Retrieved 2023-04-26.
  5. "#NigeriaElections2023: LP Abia Reps winner dedicates victory to God". Punch Newspapers (in Turanci). 2023-02-27. Retrieved 2023-04-26.