Jump to content

Odunayo Olagbaju

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Odunayo Olagbaju
Rayuwa
Haihuwa Najeriya
ƙasa Najeriya
Mutuwa 2001
Yanayin mutuwa kisan kai (stab wound (en) Fassara)
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Alliance for Democracy (en) Fassara

Odunayo Omobolanle Olagbaju dan siyasar Najeriya ne wanda ya kasance ɗan majalisar dokokin jihar Osun. An kashe shi a watan Disamba 2001[1] a gaban ofishin ƴan sanda a Ile Ife, Najeriya.[2] A watan Mayun 2002, an gurfanar da mutane goma sha ɗaya da ake zargi da aikata kisan. A watan Agusta kuma, an kama wasu mutane bakwai da ake zargi. A ƙarshen shekara ta 2002, an bayar da belin mutanen goma sha ɗaya, amma ana ci gaba da bincike kan lamarin.[3]

Kashe-kashe

[gyara sashe | gyara masomin]

Odunayo Olagbaju dai ya mutu da rana a garinsa na Ile-ife, lamarin da ya haifar da tarzoma inda aka ce aƙalla mutane biyar sun mutu.[4] Waɗanda suka mutun sun haɗa da shugaban ƙungiyar Alliance for Democracy (AD).[5] Mai magana da yawun al’ummar Ife, Prince Olakunle Aderemi, ya ce Olagbaju ya ambaci wani kwamishina a majalisar ministocin Akande, dan majalisar wakilai da kuma ɗan majalisar dokokin jihar da alhakin kai harin kafin ya mutu “a kofar ofishin ƴan sandan Najeriya, Moore, Ile-Ife”.[6]

Dalilin kashe-kashe

[gyara sashe | gyara masomin]

Kisan dai na iya kasancewa yana da alaƙa ne da taƙaddama tsakanin gwamna Bisi Akande na jihar Osun da mataimakin gwamna Iyiola Omisore. Odunayo Olagbaju ya kasance mai goyon bayan Iyiola Omisore. Kisan ya biyo bayan wasu ‘yan kwanaki da kashe mai goyon bayan Bisi Akande, Bola Ige, ministan shari’a na Najeriya. Bayan wani taron gaggawa da majalisar ministocin ƙasar ta yi, gwamnatin Najeriya ta tura sojoji domin hana afkuwar tashin wani hankalin a gaba.[7]

Ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi da kisan, Bola Ige ya ce Iyiola Omisore ya kasance ya na kusa da Olagbaju, lokacin da ya rubuta wani ɓangare bayanai na kuɗaɗen yaƙin neman zaɓe. A wani lokaci a shekarar 2001, Iyiola Omisore ya shaida wa Odunayo Olagbaju cewa ya tsallaka zuwa jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), wadda za ta mara masa baya a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar Osun. Odunayo Olagbaju da dukkan magoya bayan Omisore suma sun tsallake rijiya da baya.[8] A watan Agustan 2003, Cif Joseph Obadare na jam’iyyar PDP ya ce Olagbaju ya sanar da ƴan sanda game da barazanar da ake yi masa a rayuwarsa amma ƴan sandan sun ki su kawo masa ɗauki kafin masu kashe shin su far masa.[9]

Hukunci da saki

[gyara sashe | gyara masomin]

Mutanen biyu da aka samu da hannu a kisan sun nemi afuwa ga gwamnan jihar Osun Mista Rauf Aregbesola, a yayin cikar sa shekara guda kan ƙaragar mulki.[10]

  1. "Some Cases of Unresolved Assassinations in Nigeria (1986-2006) - In Memory of Uncle Bola Ige | Nigerian Muse". www.nigerianmuse.com. Retrieved 2018-11-18.
  2. "nigeria". www.hrw.org. Retrieved 2018-11-18.
  3. "2002 Country Reports on Human Rights Practices: Nigeria". US Department of State. March 31, 2003. Retrieved 2009-11-07.
  4. "Nigeria's Justice Minister Killed". CBS News. Dec 24, 2001. Retrieved 2009-11-07.
  5. "Vol. 15, No. 9 (A) – April 2003" (PDF). Human Rights Watch. Retrieved 2009-11-07.
  6. Razaq Yusuf & Hammed Bodunrin (2002-01-16). "Ige: Ooni's Hands Are Clean - Ife Community". This Day. Archived from the original on 2005-11-22. Retrieved 2009-11-07.
  7. "Emergency Declared in Nigeria After Killing of Justice Minister". New York Times. December 25, 2001. Retrieved 2009-11-07.
  8. Godwin Ifijeh; Chistian Ita; Hammed Bodunrin; Chuks Akunna (2002-01-15). "Suspect: Omisore Plotted Ige's Murder". This Day. Archived from the original on 2005-11-27. Retrieved 2009-11-07.
  9. Sina Babasola (August 27, 2003). "PDP alleges plot to kill Omisore". Vanguard. Archived from the original on 2011-09-29. Retrieved 2009-11-07.
  10. Sina Babasola (December 12, 2003). "Oyo House Majority Leader raises alarm over assassination plans". Vanguard. Archived from the original on 2012-02-19. Retrieved 2009-11-07.