Oloyede Adeyeoba
Oloyede Adeyeoba | |
---|---|
Rayuwa | |
Sana'a |
Oba Oloyede Adeyeoba, Akinghare ll is the current Arujale Ojima of Okeluse,Ondo State,Nigeria. Shi, ne sarkin gargajiya na Okeluse.Adeyeoba wani sarki ne na masarautar Okeluse,karamar hukumar, Ose a jihar Ondo.Yana da shekaru sha shida,ya gaji mahaifinsa,Marigayi Oba Akinghare I,Adeyeoba Omomogbe kan karaga a shekarar 2019.Ya sauke karatu daga makarantar sakandare a watan Agusta 2022.
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin 2022,Oloyede Adeyeoba ya gama karatunsa na sakandare a Greater Tomorrow International College,Arigidi,Ondo,Nigeria. A yanzu haka yana karatun Kimiyyar Siyasa a Jami'ar Afe Babalola don yin Digiri na B.Sc.
Zabi da nadin sarauta
[gyara sashe | gyara masomin]Ya zama sarki a watan Fabrairun 2019,bayan rasuwar mahaifinsa.An nada shi ya gaji mahaifinsa kasancewar namiji daya tilo da mahaifinsa ya haifa,bisa ga al'adar garinsu,an nada dan sarki na farko a matsayin wanda zai gaje shi.
Rayuwa ta sirri
[gyara sashe | gyara masomin]Akinghare ll bai yi aure ba amma yana shirin auren mace fiye da ɗaya kamar yadda al'adarsa ta tanada.