Our Beautiful Days

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Our Beautiful Days
Asali
Lokacin bugawa 1955
Asalin suna أيامنا الحلوه
Asalin harshe Egyptian Arabic (en) Fassara
Ƙasar asali Misra
Characteristics
Genre (en) Fassara romantic comedy (en) Fassara da musical film (en) Fassara
During 120 Dakika
Launi black-and-white (en) Fassara
Direction and screenplay
Darekta Helmy Halim
'yan wasa
External links

Kyawawan Ranakunmu Ko Mafi Kyawun Kwanakin Mu ( Egyptian Arabic أيامنا الحلوة, fassara. Ayyamna al-Holwa) wani fim ne na soyayya/kiɗa na Masar da aka shirya shi a shekara ta 1955 wanda darektan fina-finan Masar kuma marubuci Helmy Halim ya bada umarni kuma ya rubuta tare.[1] Taurarin fim ɗin sune: Abdel Halim Hafez, Ahmed Ramzy, Omar Sharif, da Faten Hamama. A cikin shekarar 1996, a lokacin ƙarni na Cinema na Masar, an zaɓi wannan fim ɗin a ɗaya daga cikin mafi kyawun fina-finai 150 na Masarawa.[2]

Labarin fim[gyara sashe | gyara masomin]

Faten Hamama tana wasa da Hoda, wata ‘yar talaka wacce ta bar gidan marayu ta zauna tare da samari uku (Ahmed, Ali, da Ramzi) a ɗaki a saman bene. Su uku daga cikin wadannan mutane sun so ta, amma ta fi son Ahmed, wanda Omar Sharif ke wasa, sauran kuma sun yarda da hakan kuma sun kasance da aminci ga abokantakar su. Lokacin da, wata rana, Hoda ya yi rashin lafiya, mutanen uku sun yi aiki tukuru don tattara isasshen kuɗi don biyan kuɗin tiyata. Fim ɗin bai ƙare ba game da abin da ya faru da Hoda, amma ya kamata ta zauna tare da ciwonta har tsawon rayuwarta kuma ba za ta iya aiki ko yin aure ba. Abin da fim ɗin ya nuna shi ne soyayya da ‘yan uwantaka da ke samuwa a cikin kawayenta ta hanyar rashin lafiyarta.

Manyan 'yan wasa[gyara sashe | gyara masomin]

  • Faten Hamama a matsayin Hoda
  • Omar Sharif a matsayin Ahmed
  • Abdel Halim Hafez a matsayin Ali
  • Ahmed Ramzy a matsayin Ramzy
  • Zahrat El-Ola a matsayin salwa
  • Zeinat Sedki a matsayin zanouba

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Film summary" (in Arabic). Faten Hamama's official site. Retrieved 2007-01-29.CS1 maint: unrecognized language (link)
  2. "Film summary" (in Arabic). Adab wa Fan. Archived from the original on 2007-09-29. Retrieved 2007-01-29.CS1 maint: unrecognized language (link)