Oussama Abdeldjelil

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Oussama Abdeldjelil
Rayuwa
Haihuwa Remchi (en) Fassara, 23 ga Yuni, 1993 (30 shekaru)
ƙasa Aljeriya
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Red Star F.C. (en) Fassara-
 
Muƙami ko ƙwarewa Ataka

Oussama Abdeldjelil (an haife shi a shekara ta 1993), shi ne ɗan wasan ƙwallon ƙafa na ƙasar Aljeriya wanda ke buga wasan gaba a ƙungiyar Seden a gasar cin kofin ƙasa na Faransa Championnat National.[1]

Aikin kulob[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Abdeldjelil a Algeria, kuma ya koma ƙasar Faransa yana ɗan shekaru 6. Ya fara buga ƙwallon ƙafa tare da ƙungiyoyin gida Belligny da FC Villefranche [2] kafin ya koma ƙungiyoyin ƙwararru a Faransa da Aljeriya.[3]

A ranar 8 ga Janairun shekarar 2019, Abdeldjelil ya rattaba hannu a matsayin kwararren ɗan wasa tare da ƙungiyar Red Star FC Mai buga gasar Ligue 2 ta Faransa, bayan fara kakar wasa a matsayin wanda ya fi zura ƙwallaye a gasar Championnat National tare da SO Cholet.

Ya buga wasansa na farko a matsayin kwararre tare da Red Star a cikin nasara da ci 1-0 a Ligue 2 akan RC Lens a ranar 14 ga Janairun 2019 yana zira ƙwallaye ɗaya da cin nasara.[4]

A lokacin rani na shekarar 2019, Abdeldjelil ya rattaba hannu a ƙungiyar Paris FC makwabciyarta ta Ligue 2 bayan da Red Star ta fadi a karshen kakar 2018-19 Ligue 2 . Ba tare da zira ƙwallaye a wasanni 14 ba, ya bar kulob ɗin ya koma Cholet a cikin Janairun 2020.[5]

A watan Yunin 2020, tsohon darektan wasanni na Orléans Anthar Yahia ya dauki Abdeldjelil, don bugawa USM Alger a cikin ƙasar haihuwarsa.[6]

A ranar 31 ga Janairun 2021, Abdeljelil ya rattaba hannu a ƙungiyar Championnat ta Faransa US Boulogne kan kwantiragi har zuwa ƙarshen kakar wasa ta bana, bayan da ya ƙare kwantiraginsa da USM Alger. Wasu majiyoyi sun ce ya ci ƙwallo ukku rigis a farkon wasan sa a kulob ɗin, a wasannin zagaye na takwas na gasar Coupe de France ranar 16 ga watan Fabrairun 2021, ko da yake wasu majiyoyi a lokacin sun ba da ƙwallo ta uku a matsayin ƙwallon da abokan karawa su ka ci gidansu da kansu-(own goal). [7][8][9]

Ayyukan kasa da kasa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Abdeldjelil a Aljeriya, kuma ya wakilci Aljeriya U23 don samun cancantar shiga gasar Olympics .[10]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Oussama ABDELDJELIL, 1ère recrue". Archived from the original on 2020-07-16. Retrieved 2023-04-06.
  2. "Oussama Abdeldjelil, l'arme fatale du SO Cholet". 25 October 2018.
  3. "Ligue 2 : Oussama Abdeldjelil, un serial buteur au Red Star". leparisien.fr. 13 January 2019.
  4. "Red Star FC - RC Lens (1-0) - Saison 2018/2019 - Domino's Ligue 2". www.lfp.fr.
  5. "Mercato – Oussama Abdeldjelil va quitter le Paris FC pour le National 1" (in Faransanci). maligue2.fr. 22 January 2020.
  6. "Oussama Abdeldjelil quitte Cholet pour un nouveau challenge" (in Faransanci). actufoot.com. 19 June 2020.
  7. "Oussama Abdeldjelil's hat-trick propels US Boulogne past Lambresienne in French Cup". goal.com. 16 February 2021.
  8. "Boulogne vs. Lambresienne 5-0". Soccerway. 16 February 2021.
  9. "US Boulogne CO 5-0 ES Lambres" (in Faransanci). FFF.fr. 16 February 2021.
  10. farid (11 October 2015). "Interview: Oussama Abdeldjelil, AS Saint Priest (EN-Algérie espoir)".

Hanyoyin haɗi na waje[gyara sashe | gyara masomin]

  • Oussama Abdeldjelil at Soccerway
  • Oussama Abdeldjelil – French league stats at Ligue 2 (in French) – English translation