Jump to content

Paula Francisco Coelho

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Paula Francisco Coelho
Minister of Environment of Angola (en) Fassara

26 Satumba 2017 - 17 ga Janairu, 2020
Rayuwa
Haihuwa Luanda, 7 ga Yuli, 1981 (43 shekaru)
ƙasa Angola
Karatu
Makaranta Jami'ar Fasaha ta Tshwane
Harsuna Portuguese language
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da environmentalist (en) Fassara
Wurin aiki Luanda
Imani
Jam'iyar siyasa People's Movement for the Liberation of Angola (en) Fassara

Paula Cristina Francisco Coelho (an haife ta a ranar 7 ga watan Yuli, 1981) an naɗa ta ministar muhalli ta Jamhuriyar Angola a watan Satumba na 2017 ƙarƙashin gwamnatin João Lourenço.[1] Kafin ta zama Ministar Muhalli, ta kasance Sakatariyar Kula da Dabbobi da Kare halittu[2] Ta fara aikinta da ma’aikatar muhalli a matsayin mai fasaha, daga baya ta zama Darakta mai kula da halittu na ƙasa.[3]

Yayin da take da gogewa wajen tunkarar ƙalubalen muhalli a Angola,[4] ta tsara ayyuka da dama da suka shafi bambancin halittu, sauyin yanayi, sarrafa shara, kiyaye ƙasa da ruwa. Paula Francisco tana da digiri na farko a cikin kula da wuraren kariya daga Jami'ar Fasaha ta Tshwane, Afirka ta Kudu. An haife ta a Luanda, mamba ce mai ƙwazo a cikin kwamitin tsakiya na ƙungiyar jama'a da 'yantar da Angola kuma na Ƙungiyar Mata ta Angolan.

Abubuwan da suka sa gaba a cikin aikinta su ne ilimin muhalli, sarrafa sharar gida da kuma karfafa manufofin da suka shafi namun daji.[5]

  1. Vaga, Nova. "João Lourenço já formou Governo - Saiba quem são os novos ministros e governadores". Novo Jornal (in Harshen Potugis). Retrieved 2018-06-05.
  2. "Mais investimento para salvar palanca negra gigante da extinção". Portal de Angola (in Harshen Potugis). Retrieved 2018-06-05.[permanent dead link]
  3. "Presidente da República nomeia secretários de Estado". ANGOP (in Harshen Potugis). Retrieved 2018-06-05.
  4. "MPLA". www.mpla.ao (in Harshen Potugis). Archived from the original on 2018-10-02. Retrieved 2018-06-05.
  5. "Ministra do ambiente elege educação ambiental como prioridade". ANGOP (in Harshen Potugis). Archived from the original on 2018-07-13. Retrieved 2018-06-05.