Pavlo Vyshebaba

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Pavlo Vyshebaba
Rayuwa
Haihuwa Kramatorsk (en) Fassara, 28 ga Maris, 1986 (38 shekaru)
ƙasa Ukraniya
Karatu
Makaranta Mariupol State University (en) Fassara 2012) specialist (en) Fassara : Journalism
Sana'a
Sana'a mawaƙi, social activist (en) Fassara da animal rights advocate (en) Fassara

Pavlo Oleksandrovich Vyshebaba (an haife shi a watan Maris 28, 1986, Kramatorsk, yankin Donetsk, Ukrainian SSR) ɗan fafutukar kare muhalli ne, mawaƙi kuma marubuci. Tare da shi aka kafa kuma shine shugaban "One Planet" NGO, UNDP kungiya dake wakilincin juriya a Ukraine. [1]

Tarihin Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Pavlo Vyshebaba a Kramatorsk. Ya fara karatun injiniyanci a makarantar Donbas Machine-Building Academy, amma bayan shekara ta uku ya janye takardunsa kuma ya koma karatun jarida a Jami'ar Jihar Mariupol.[2] A lokacin da yake karatu, ya yi aiki na tsawon shekaru uku a gidan jaridar "Priazovsky rabochy".

A shekara ta 2012, bayan kammala karatunsa da kyaututuka daga jami'a, ya koma Kyiv. Ya taka rawa sosai a cikin juyin juya halin mutuntaka wato Revolution of Dignity, musamman ayyukansa na cibiyar yada labarai na hedikwatar Resistance ta kasa. Bayan hambarar da gwamnatin Yanukovych, ya yi aiki na tsawon shekara daya da rabi a kafar labarai ta majalisar ministocin kasar Ukraine, yana aiki na sadarwa da huldodin kasa da kasa tsakanin ma'aikatu.

Ya ƙi yarda yayi amfani da harshen Rashanci, ya canza zuwa Ukraniyanci, yana jayayya cewa wannan aikin na Kramatorsk ne ta hanyar "'yan bindigar Rasha da masu haɗin gwiwa".[3]

Acikin shekara ta 2013, ya zama mai cin kayan ganye kadai, a cikin 2015 ya zama mai cin ganyayyaki, a ƙarshe ya bar cin dabbobin teku da tufafin da aka yi daga dabbobi[3]. A Afrilu 13, 2016, ya bude wurin cin abincin ganye na farko a Ukraine "One Planet". A cikin watan Agusta na wannan shekarar, ya yanke shawarar samun ƙungiyar makaɗa da za suyi waka na musamman don jituwar dan Adam da muhallinsa na zahiri.

A lokacin bazara na shekara ta 2017, "One Planet Orchestra" ya tattara fiye da wakoki dubu 45 a dandalin taro na jama'a mai suna "Spilnokost", [4] inda ta zamo gungun mawaka na farko da suka taba karbar tallafi daga jama'a don yin waka. [5]

Abubuwa masu ban sha'awa[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin wata hira, Pavlo Vyshebaba ya sanya sunan Mahatma Gandhi da Nelson Mandela a matsayin wadanda ya ke kwaikwayo na daga dabi'unsa, kuma a cikin shahararrun mutanen Ukraine ya zabi Hryhoriy Skovoroda da Taras Shevchenko. Lokacin yaro, Vyshebabu ba a shigar da shi a makarantar kiɗa na Kramatorsk ba, yana lura da cewa ba shi da damar yin kida. [6]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]