Petros Mhari
Petros Mhari | |||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||
Haihuwa | Filabusi (en) , 1989 (34/35 shekaru) | ||||||||||||||||||
ƙasa | Zimbabwe | ||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||
|
Petros Mhari (an haife shi ranar 15 ga watan Afrilu, 1989) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Zimbabwe wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron gida ga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta FC Platinum ta Zimbabwe, da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Zimbabwe.
Sana'a/Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Mhari ya tafi makarantar motsa jiki a makarantar sakandare ta Shangani, kuma asalinsa yana buga wasan tsakiya. An tilasta masa yin wasan ƙwallon hannu a makaranta saboda ƙarancin ɗalibai masu sha'awar, amma daga can ya koyi dabarun da ke fassara zuwa matsayin mai tsaron gida a ƙwallon ƙafa. Ya fara babban aikinsa a matsayin mai tsaron gida tare da Shabanie Mine, kafin ya koma Hwange Colliery a shekara ta (2009). A cikin shekarar (2013) ya koma FC Platinum inda ya taimaka wa ƙungiyarsa ta lashe kofunan gasar ƙwallon ƙafa ta Zimbabwe (3) a jere daga shekara ta (2017 zuwa shekara ta 2019).[1]
Ayyukan kasa
[gyara sashe | gyara masomin]Mhari ya fara buga wasansa na farko na kasa da kasa tare da tawagar kasar Zimbabwe a ci (1-0) a shekara ta (2022) na cancantar shiga gasar cin kofin duniya na FIFA a Afrika ta Kudu a ranar (11) ga watan Nuwamba a shekara ta (2021).[2] Ya kasance cikin tawagar 'yan wasan Zimbabwe a gasar cin kofin Afrika na shekarar (2021).[3]
Girmamawa
[gyara sashe | gyara masomin]FC Platinum
- Kofin Zimbabwe : 2014
- Gasar ƙwallon ƙafa ta Zimbabwe : 2017, 2018, 2019
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]Hanyoyin haɗi na waje
[gyara sashe | gyara masomin]- Petros Mhari at National-Football-Teams.com
- Petros Mhari at Soccerway