Jump to content

Peugeot 406

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Peugeot 406
automobile model (en) Fassara
Bayanai
Mabiyi Peugeot 405 (en) Fassara
Ta biyo baya Peugeot 407
Manufacturer (en) Fassara Peugeot
Brand (en) Fassara Peugeot
Location of creation (en) Fassara PSA Sochaux Plant (en) Fassara

Peugeot 406 babbar motar iyali ce mai tuƙi ta gaba wacce kamfanin kera motoci na Faransa Peugeot ya kera tsakanin 1995 zuwa 2004. Akwai tsarin salon estate da coupé wacce ke da zabin man fetur ko injin turbodiesel wato injin din dake daukar diesel. 406 ta maye gurbin Peugeot 405 a cikin layin Peugeot, kuma an maye gurbinta da Peugeot 407 wacce akayi bayan an kammala ta.

Tsarin Aiki

[gyara sashe | gyara masomin]

Salon na 406 yana da tasiri sosai daga magabaciyarta wato 405, wadda aka fara cirewa daga ƙaddamarwa bayan fitowar 406 a watan Satumbar 1995, kuma a ƙarshe aka daina kera ta a Turai a cikin 1997, lokacin da aka dakatar da samfuran gidaje na ƙarshe. Cinikayyar motar a Burtaniya fara ne a cikin Fabrairu 1996. [1]

Da farko dai, akwai motar da ke daukar man fetur 1.8 L da 2.0 L da injunan turbodiesel 1.9 L, sai kuma man fetur 2.0 mai turbocharged, 2.9 (2946 cc, mai lamba 3.0) V6, da kuma mai 110. bhp 2.1 l turbodiesel . Nau'ikan diesel sun shahara sosai, kuma 406 sun zama ɗaya daga cikin manyan motocin da ake siyarwa da dizal a Turai.[ana buƙatar hujja]

  1. PEUGEOT's 406 range will arrive with a spectacular car launch campaign in Britain next year.