RFI Hausa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

RFI Hausa Gidan rediyo ne, mallakin kasar Faransa wadda take yada labaranta a harshen Hausa a duk fadin duniya. Gidan rediyon nadaga cikin sashin babban tashar rediyo ne na Rediyo Faransa wanda akafi sani da turanci da Radio France International (RFI), kuma tanada wasu bangariri na harsunan duniya daban-daban.[1]

Harshen Afrika na farko a kan babban radioyon duniya

Rfi radiyo na farko a kasashen Afrika renon Faransa, ya kara fadada shirye shiryensa ga masu sauraro, tare da bunkasa manufofinsa a nahiyar.

Daga ranar litanin 21 ga watan mayu shekara ta 2007 kai tsaye daga dakin shirya labarunsa da ked a cibiya a Muryar Nijeriya Lagos, Rfi zai watsa shirye shiryensa a cikin harshen hausa na tsawon awowi 2 a kowace rana.

A kowa ce safiya akwai shirye shirye guda biyu Daga karfe 6h TU zuwa 6h 30 TU, wato kafe 7h agogon Nijeriya, Nijer, Kamaru, da Chadi.

Da kuma karfe 7h TU zuwa 7h30 TU, wato kafe 8h zuwa 8h zuwa 8h30 a gogon Najeriya, Nijer, Kamaru da Chadi.

Tare da shirin awa guda a kowane yammaci, da misalin karfe 4h zuwa 5h TU wato karfe 5h zuwa 6h a gogon Najeriya, Nijer Kamaru da Chadi.

Nahiya Afrika dai na kunshe da kimanin mutane Miliyo 80 da ke magana a cikin harshen hausa, wadanda Rfi ked a burin gabatar masu da shirye shiryensa, tare da nunu kwarewarsa wajen bada labaran da su ka shafi duniya da kuma na nahiyar Afrika.

A Nijer za a iya kama mu ne kan mita 96.2 zangon FM a biranen: Niamey – Maradi – Zinder – Tahoua.

A sauran sassan duniya kuma za a iya kama mu a kan mita 19 da 41 gajeren zango.

Anazarci[gyara sashe | Gyara masomin]

  1. http://www.hausa.rfi.fr/ nagai she ku [rfi-hausa] www.hausa.rfi.fr