Raƙumi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Raƙumi
07. Camel Profile, near Silverton, NSW, 07.07.2007.jpg
Scientific classification
KingdomAnimalia
PhylumChordata (en) Chordata
Classmammal (en) Mammalia
OrderArtiodactyla (en) Artiodactyla
DangiCamelidae (en) Camelidae
genus (en) Fassara Camelus
Linnaeus, 1758
Geographic distribution
Dromedary Range.png
Raƙumi
Raƙumma sunyi layi suna tafiya



Raƙumi a afirka.
Raƙumi

Raƙumi dai wata halittace daga cikin dabbobin da Allah maɗaukakin sarki ya halitta bisa hikima da ikonsa. Babu shakka akwai ayoyi da hikimomi masu yawa tattare da irin tsari na musamman da Allah ya keɓanci raƙumi da su. Kuma ya halicci raƙumi da su ne, domin su zamo ayoyi abin lura ga ma'abota hankali.

Kasancewa akwai zafi mai tsananin gaske a hamada, wanda ba duka halittu za su iya jurewa ba. Sannan kuma akwai ƙura haɗe da yashi da take tashi ko da yaushe, wadda take rufe duk wata halitta da ta ci karo da ita. Ga babbar halitta kuma ƙurar takan sa wahalar nunfashi da shaƙar iska. Idan ka ɗauke ƙanan halittu dangin su kadangare, raƙumi shi ne kaɗai wata ƙatuwar halitta da take iya rayuwa a cikin hamada. Kuma mahaliccin raƙumi ya halicce shi ne musamman domin ya rayu a cikin hamada, ya kuma zama mai hidima ga al'ummar dake rayuwa a wannan ɓangare.

Abu mafi muhimmanci da aka fi buƙata a hamada shi ne ruwa, domin ai maganin ƙishirwa, amma kuma abu ne mai wahalar gaske a samu ruwa a hamada. Kuma ba abu ne mai yiwuwa ba, a samu wani abinci a cikin yashin hamada. Hakan na nufin kenan duk wata dabba da zata rayu a hamada, ya zama wajibi ta zamanto tana da wata kariya daga jin ƙishirwa da kuma yunwa. Babu shakka haka abin yake ga raƙumi, domin babu wata dabba da ta fi shi jure ƙishirwa da yunwa.

Raƙumi zai iya rayuwa har na tsawon kwana takwas ba tare da ci ko sha ba. Don haka idan raƙumi ya samu inda zai sha ruwa, kasancewar yana da matuƙar buƙatarsa, sai ya sha ya kuma ajiye wani ruwan a cikinsa. Raƙumi yakan iya shan ruwan da ya kai ɗaya bisa uku na girmansa a cikin minti goma kacal, wato kwatankwacin galan 30 kenan.

Tozon raƙumi kuwa na tattare da kitsen da ya kai kilo 40. Godiya ta tabbata ga wanda ya halicci tozon raƙumi, yadda zai sa raƙumi ya yi kwanan da kwanaki a cikin hamada ba tare da cin abinci ba.

Mafiya yawan dangogin abinci da ake samu a hamada busassu ne, kuma masu tauri, amma duk da haka an tsara halittar kayan cikin raƙumi yadda za su iya narkar da kusan duk wasu nau'o'in abinci da ake samu a hamada, komai taurinsa kuwa. Mahaliccin rakumi ya halittar masa waɗansu irin haƙora yadda za su dace da abincinsa.

Babu shakka ƙurar hamada na daga cikin gararin da halittun da ke ratsa hamada ke fama da ita, saboda tana buɗe musu ido, ta kuma hana su shaƙar iska yadda ya kamata. Amma mahaliccin raƙumi ya halitta masa wata fata daga saman idonsa kamar gilashi, wadda take sakkowa yayin da iskar hamada ta taso, sai ta zama kariya ga idon. Sannan ga kuma dogon gashin ido mai kauri da yake hana tsakuwoyin yashin hamada isa ga idon raƙumin.

Har ila yau an tsara halittar hancin raƙumi yadda idan iska mai yashi ta taso zai iya manne ƙofofin hancinsa, ya riƙa shaƙar iska ta wata ‘yar kafa ta musamman mai cike da kariya, yadda babu wani yashin hamada da zai shiga cikinsa.

Ɗaya daga cikin matsalolin da abubuwan hawa ke fuskanta yayin ratsa hamada shi ne kafewa a cikin yashi. Amma irin wannan haɗari bai taɓa faruwa ga raƙumi ba, koda kuwa yana ɗauke da labtun kaya, saboda an halicci ƙafafuwan raƙumi ne musamman saboda ratsa hamada. Kasancewar kofaton raƙumi yana da wani maganaɗisu da baya barinsa ya kafe cikin yashi, saboda kofaton yana aiki ne kamar takalmin da Bature yake amfani da shi idan zai ratsa ta cikin dusar ƙanƙara. Sannan kuma doguwar ƙafarsa ta nisanta shi da tiririn zafin yashin hamada.

Jikinsa kuma na rufe shi da wata fata ta musamman, wadda take iya kare shi daga zafin rana ko kuma zafin yashi a lokacin da yake kwance. Wanna tsari na halittar raƙumi, shi ne abin da ya fito da halittar raƙumi fili, a matsayin wata cikakkiyar halitta.


Bari mu yi wa mai karatu wata tunatarwa ta musamman dangane da ɓangarorin halittar raƙumi da muka bayyana;


 • Cikakken tsarin da ya ba shi ikon jure ƙishirwa.
 • Tozonsa da ya ba shi ikon jure yunwa.
 • Ƙafafuwansa da suka bashi damar tafiya salin-alin cikin hamada.
 • Fatar kariya ta ido da take kareshi daga iskar hamada.
 • Gashin idonsa da yake kare idon daga tsakuwoyin yashin hamada.
 • Hancinsa da aka halitta da wata kariyar yashi ta musamman.
 • Tsarin bakinsa da ya ba shi ikon cin duk wani abinci a hamada.
 • Kayan cikinsa da suke narkar da duk abin da ya ci komai taurinsa.
 • Fatar cikinsa da take ba shi kariya daga tsananin zafin hamada.
 • Kofatonsa da yake kareshi daga kafewa a cikin yashin hamada.
 • Dukkan waɗannan gaɓɓai na raƙumi da muka lissafa, babu ɗaya daga cikin tsarin nan na ƙarya na juyin halitta da ya iya bayyana yadda akai *waɗannan gaɓɓai suka samu.

Saboda haka waɗannan gaɓoɓi na raƙumi da ma sauran da ba mu iya ambaton su anan ba, suna nusar da mu ne ga wata hujja tabbatacciya. Wato dai raƙumi wata ƙasaitacciyar dabbace da mahalicci ya halitta domin ya iya biyan buƙatar al'ummar da suke rayuwa a ɓangaren hamada. Wannan mahalicci kuwa shi ne Allah maɗaukaki kuma mahaliccin komai.

Tsawon kwanaki nawa raƙumi yake iya yi ba tare da ci ko sha ba