Jump to content

Ram Ouédraogo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ram Ouédraogo
Rayuwa
Haihuwa Agboville (en) Fassara, 2 ga Janairu, 1950 (74 shekaru)
ƙasa Burkina Faso
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Rally of the Ecologists of Burkina (en) Fassara

Ram Ouédraogo (an haife shi a watan Janairu 2, 1950)[1] ɗan siyasan Burkinabe ne kuma shugaban jam'iyyar Rally of the Ecologists of Burkina (RDEB).

An haifi Ouédraogo a Agboville, Cote d'Ivoire, ga iyayen Burkinabe daga Lardin Passoré . Ya tsaya takara a matsayin ɗan takarar jam'iyyar Greens for Development of Burkina (UVDB) a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ranar 15 ga watan Nuwamban ,1998, inda ya zo na biyu bayan shugaba mai ci Blaise Compaore da kashi 6.61% na ƙuri'un da aka kada. Daga baya ya bar UVDB kuma ya kafa jam'iyyar RDEB.[1]

Daga 1999 zuwa 2002, Ouédraogo yayi aiki a gwamnati a matsayin ƙaramin ministan sulhu na ƙasa.[1]

A zaɓen shugaban ƙasa na 13 Nuwamba, 2005, Ouédraogo ya sanya na biyar cikin 'yan takara 13, inda ya sami kashi 2.04% na ƙuri'un.

  1. 1.0 1.1 1.2 Page at petiteacademie.gov.bf Archived 2011-09-28 at the Wayback Machine (in French).