Raphael Nomiye

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Raphael Nomiye
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

Rayuwa
Haihuwa Ilaje, ga Faburairu, 1963
ƙasa Najeriya
Mutuwa Nuwamba, 2013
Karatu
Makaranta Jami'ar Benin
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Nigeria Labour Party

Raphael Nomiye (Fabrairu 1963 - Nuwamba 2013) ɗan siyasar Najeriya ne kuma ɗan majalisa a majalisar wakilai ta Najeriya, mai wakiltar Ilaje dake Ese Odo na Tarayyar Jahar Ondo, Nigeria.[1][2]

Rayuwar farko[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Nomiye ne a ranar 6 ga watan Fabrairun 1963, a garin Ugbo, cikin ƙaramar hukumar Ilaje a jihar Ondo, a kudu maso yammacin Najeriya.[3] Ya halarci Kwalejin Kasuwancin Kings da ke Jihar Ribas da ke Kudancin Najeriya kafin ya samu digiri na farko a fannin harkokin gwamnati a Jami’ar Benin da ke Jihar Edo.[4]

Rayuwar Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin shekarar 2011, jam'iyyar Labour ta Najeriya ta tsayar da shi takarar kujerar mazaɓarsa ta Ilaje da Ese Odo a Mazaɓar tarayya ta jihar Ondo, Najeriya,[5] wanda ya lashe zaɓen. Ya zauna a wannan kujera har zuwa rasuwarsa a cikin watan Nuwamban 2013.[6][7]

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

  • Zaɓen fidda gwani na Ilaje-Ese Odo

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://web.archive.org/web/20150402174034/http://www.tribune.com.ng/niger-delta/item/1102-ondo-bye-election-brothers-at-war/1102-ondo-bye-election-brothers-at-war
  2. https://web.archive.org/web/20150402125544/http://www.nigeriancurrent.com/ck88-news/raphael-nomiye-50-ondo-house-of-reps-lawmaker-slumps-dies
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2016-03-04. Retrieved 2023-03-18.
  4. https://saharareporters.com/2013/11/23/federal-rep-ondo-dies-apparent-heart-attack
  5. https://en.wikipedia.org/wiki/Raphael_Nomiye
  6. https://web.archive.org/web/20131130032149/http://www.thisdaylive.com/articles/nomiyes-death-stalls-onwuliri-oduahs-appearance-before-house-of-reps/165316/
  7. https://web.archive.org/web/20160305043221/http://m.nationalmirroronline.net/article/decision-day-in-ilaje-ese-odo-federal-constituency