Jump to content

Richard Gbande

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Richard Iorkyaan Gbande ɗan siyasan Najeriya ne wanda ya taba zama memba mai wakiltar Katsina-Ala/Ukum/Logo a majalisar wakilai. An haife shi a shekarar 1972, ya fito ne daga jihar Benue. Ya gaji Memga Emmanuel kuma an zaɓe shi a shekarar 2019 a matsayin ɗan majalisar wakilai ta ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP). [1] Ya baiwa al’ummar mazaɓar sa sama da Naira miliyan 100 da kayayyaki domin inganta rayuwarsu. [2] An dakatar da shi daga jam’iyyarsa ne saboda rashin biyayya. [3]

  1. "Citizen Science Nigeria". citizensciencenigeria.org (in Turanci). Retrieved 2025-01-06.
  2. Okogba, Emmanuel (2022-05-27). "Benue Reps, Gbande distributes empowerment items to constituents". Vanguard News (in Turanci). Retrieved 2025-01-06.
  3. "PDP suspends Suswam, others over 'insubordination' - Daily Trust". Daily Trust (in Turanci). 2024-08-08. Retrieved 2025-01-06.