Jump to content

Rosa Gala

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Rosa Gala
Rayuwa
Haihuwa Lubango, 17 ga Afirilu, 1995 (29 shekaru)
ƙasa Angola
Karatu
Harsuna Portuguese language
Sana'a
Sana'a basketball player (en) Fassara
Itinerary
Ƙungiyoyi Shekaru Pos Nbr
C.D. Primeiro de Agosto (en) Fassara-
 
Muƙami ko ƙwarewa small forward (en) Fassara
Rosa maria

Rosa Maria Luísa Gala (an Haife ta ranar goma sha bakwai 17 ga watan Afrilu, shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da casa'in da biyar 1995) ƙwararriyar ƴar wasan kwando ce ƴar ƙasar Angola.[1]

An haife ta a Lubango, an zaɓi Gala don buga wa tawagar ƙwallon kwando ta mata ta Angola wadda ta lashe tagulla a gasar FIBA ta Afirka ta matasa ƴan ƙasa da shekaru goma sha shida 16 na shekara ta alif dubu biyu da goma sha ɗaya 2011. a shekara ta gaba an zaɓe ta a shekarar alif dubu biyu da goma sha biyu 2012 FIBA Africa Championship Ƙasa da ƴan shekaru goma sha takwas U-18. An zaɓe ta ne a cikin tawagar ƴan wasan ƙwallon kwando ta mata ta Angola domin shiga gasar Afrobasket ta shekarar alif dubu biyu da goma sha ukku 2013 amma daga baya aka kore ta saboda ta kasa cika ƙa’idojin shekaru.[2]

Ƙungiyar Gala ta Gala, CD Primeiro de Agosto, ta zo na biyu a gasar cin kofin zakarun ƙungiyoyin mata na FIBA na shekarar dubu biyu da goma sha ukku 2013. Ta sake wakilci Angola a wasan ƙwallon kwando a gasar Lusophony na shekarar dubu biyu da goma sha huɗu 2014, inda ta lashe azurfa. Ta kuma yi wa Angola wasa a gasar cin kofin duniya ta FIBA ta mata a cikin shekarar alif dubu biyu da goma sha huɗu 2014 da kuma wasan ƙwallon kwando a gasar wasannin Afrika – gasar mata ta shekarar dubu biyu da goma sha biyar 2015.

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2016-03-03. Retrieved 2023-03-30.
  2. http://www.portalangop.co.ao/angola/pt_pt/noticias/desporto/2013/7/32/Anibal-Moreira-indica-atletas-para-estagio-Espanha,eeec62f3-f76d-4235-88af-7aa246a27f98.html