Ruwa (gari)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ruwa

Wuri
Map
 17°53′23″S 31°14′41″E / 17.8897°S 31.2447°E / -17.8897; 31.2447
JamhuriyaZimbabwe
Province of Zimbabwe (en) FassaraMashonaland East Province (en) Fassara
Yawan mutane
Faɗi 22,038 (2002)
Labarin ƙasa
Altitude (en) Fassara 1,562 m
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
UTC+02:00 (en) Fassara

Ruwa, wani gari ne a lardin .Mashonaland ta Gabas, Zimbabwe, mai tazarar kilomita 22 daga kudu maso gabas da Harare babban birnin ƙasar Zimbabwe a kan babbar hanyar Harare zuwa, Mutare da layin dogo.[1]

Dubawa[gyara sashe | gyara masomin]

Garin na aiki a matsayin ƙaramar cibiyar gudanarwa da kasuwanci na kewayen yankin noma. A cikin shekarun baya-bayan nan garin ya bunƙasa cikin sauri kuma ya zama yanki mai farin jini ga mutanen da ke ƙaura daga birnin Harare.

Cibiyar Gyaran garin Ruwa da ke wajen garin an kafa ta ne a shekarar 1981 domin farfado da naƙasassu tsoffin mayakan.

Wurin shaƙatawa na garin, Scout Park wanda ya karɓi baƙuncin Jamboree ta Tsakiyar Afirka a 1959 yana nan kusa.

Garin Ruwa ya faɗa cikin mazaɓar Seke kuma a zaben 2005 na majalisar wakilai ya zabi Phineas Chihota da kuri'u sama da 6000.

Ganin UFO[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin 1994, an ba da rahoton cewa makarantar Ariel da ke gsrin ta kasance wurin da aka ga wata ƙasa ta UFO. Wasu daga cikin ɗalibai kusan 60 da abin ya faru kuma sun ba da rahoton cewa wani “bakon halitta” ya yi magana da su. A cewar daliban, da John E. Mack ya yi hira da su a rukuni, an gargade su da su kula da yanayin.[2] [3]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Harare". Zimbabwe Government Portal.
  2. Ariel Phenomenon: Encounter in Ruwa – The Ariel School UFO Sighting Documentary
  3. Exploring African and Other Alien Encounters by John E. Mack

17°53′23″S 31°14′41″E / 17.88972°S 31.24472°E / -17.88972; 31.24472