Sabo Nanono

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sabo Nanono
Minister of Agriculture and Rural Development (en) Fassara

21 ga Augusta, 2019 - 1 Satumba 2021 - Muhammad Mahmood Abubakar
Rayuwa
Haihuwa 11 ga Afirilu, 1946 (78 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Sabo Nanono (an haife shi a 11 ga Afrilu, 1946) ɗan siyasar Najeriya ne. Ya riƙe muƙamin Ministan Noma da Raya Karkara da Shugaba Muhammadu Buhari ya naɗa har zuwa lokacin da aka kore shi a ranar 1 ga watan Satumba a shekara ta 2021.[1][2][3]

Tarihi da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Nanono a ranar 11 ga watan Afrilu, 1946 a Tofai, Gabasawa, Jihar Kano. Yana da aure kuma yana da ƴaƴa da yawa. Ya samu shaidar kammala karatunsa na farko a makarantar firamare ta Gwarba jihar Kano sannan ya samu shaidar kammala karatunsa na babbar sakandare a makarantar gwamnati ta Kano. A shekara ta 1972, Nanono ya samu digirin farko a fannin harkokin kasuwanci daga jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya kuma digiri na biyu a fannin manufofin jama’a da gudanar da mulki daga jami’ar Wisconsin-Madison a shekarar 1977. Bayan haka a shekarar 1994, ya halarci kwas na Advanced Management a Harvard Business School a Boston.[4][5][6]

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Nanono ya fara aiki a matsayin magatakarda a babban bankin Najeriya a jihar kano. A shekarar 1972 ya zama jami’in tsare-tsare a gwamnatin jihar Kano. Nanono yayi aiki a matsayin malamin jami'a daga shekara ta 1973 zuwa 1978. A watan Yulin 1978, ya yi aiki da Kamfanin Raya Najeriya a matsayin Babban Jami'in Zuba Jari. Daga shekarar 1980 zuwa 1983, Nanono ya riƙe muƙamin Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Kamfanin Zuba Jari da Ƙadarori na Jihar Kano. Bayan haka, Nanono ya zama ma’aikacin Banki wanda daga baya ya kai matsayin Manajan Darakta kuma Shugaban Babban Bankin Duniya na African International Bank Limited. Sabo Nanono ya yi aiki da wasu ƙungiyoyi kafin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa shi ministan noma da raya karkara.[5][6][7]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://www.bloomberg.com/profile/person/21581408
  2. https://www.premiumtimesng.com/news/headlines/347816-full-list-portfolios-of-buharis-44-ministers-2019-2023.html?tztc=1
  3. https://gazettengr.com/just-in-buhari-sacks-power-minister-saleh-mamman-agric-minister-sabo-nanono/
  4. https://fmard.gov.ng/hma/
  5. 5.0 5.1 https://pmnewsnigeria.com/2021/04/08/buharis-74-year-old-minister-nanono-marries-18-year-old-girl/?__cf_chl_managed_tk__=pmd_a01329c58bc3b7d483338ae2d3b61350dab75644-1628152878-0-gqNtZGzNAw2jcnBszQf6
  6. 6.0 6.1 "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-08-10. Retrieved 2023-03-14.
  7. https://blerf.org/index.php/biography/nanono-alhaji-mohammed-sabo/