Saburi Adesanya
Saburi Adesanya Addjimi masanin babbar makaranta ne a Najeriya, marubuci kuma babban mataimakin shugaban jami'ar Olabisi Onabanjo na bakwai. Ya taba zama mataimakin shugaban riko kafin a tabbatar da shi a shekarar dubu biyu da sha biyar (2015). Ya bar ofishin ne a shekarar dubu biyu da sha bakwai (2017) bayan ya shafe shekaru biyar yana hidima.
Makarantun da ya Halarta
[gyara sashe | gyara masomin]Farfesa Adeyemi ya halarci Makarantar Grammar Baptist dake Ibadan tsakanin 1966 zuwa 1970, sannan ya wuce Kwalejin Igbobi dake Legas daga 1971 zuwa 1972. Daga nan sai ya tafi Jami’ar Ibadan a shekarar 1973 inda ya samu digiri na farko a fannin kimiyyar halittu a shekarar 1976. Ya sake zuwa Jami'ar Obafemi Awolowo inda ya yi karatun M.Phil. (A fannin magungunan da ka samar daga itatuwa) a cikin 1981. [1]