Jump to content

Sadi Sidi Sharifai

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Sadi Sidi Sharifai mawaki ne a masana'antar fim ta Hausa wato Kannywood ya Dade a masana'antar Yana Wakokin soyayyah Dana bege, Yana Wakokin Siyasa kuma.[1]

Takaitaccen Tarihin Sa

[gyara sashe | gyara masomin]

Cikakken sunan sa shine sadi sidi sharifai. An haife shi a watan nuwamba shekarar 1980 a Karamar hukumar dala Dake kano. Mawaki ne a masana'antar kanniwud sannan aboki ga manyan jarumai uku Yakubu muhammad, Sani Danja, da Kuma margayi Rabilu Musa. Shine fitaccen mawaki tun shekarar 2005. Danae ga Alhaji sidi sharifai sarkin sharifan kano na darikar tijjaniyya. Babban Amini ne ga maragayi jarumi Rabilu Musa Idris, Yana da kamfanin Ar-rahuz entertainment. [2]Ya fito a fina finai kamar haka.[3]

  • Daga Allah
  • Dan Kuka
  • ibro ko Dania
  • Mai dawa
  • yankan baya
  1. https://www.projectreserve.com/2018/06/nazarin-jigogin-waoin-soyayya-na-sadi.html?m=1
  2. https://www.360hausa.com.ng/music-sadi-sidi-sharifai-maraici-mp3-download/
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-31. Retrieved 2023-07-31.