Jump to content

Sadiq Abdulkarim Abdulrahman

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sadiq Abdulkarim Abdulrahman
Rayuwa
Haihuwa 1966 (57/58 shekaru)
Sana'a
Sana'a likita da ɗan siyasa

Sadiq Abdulkarim Abdulrahman likita ne kuma ɗan siyasan Libya wanda ya yi aiki a matsayin mataimakin firaminista na farko tsakanin 14 ga watan Nuwamba shekara ta 2012 da kuma ranar 29 ga watan Agusta shekara ta 2014.

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Abdulrahman a wajajen shekara ta 1966. Ya sami digiri na farko a babban aikin tiyata a shekarar 1993. Sannan ya sake karatun digiri na biyu a fannin likitanci a shekara ta 2001 sannan ya sake yin karatun digirin-digirgir a fannin likitanci a shekara ta 2005.

Abdulrahman yayi aiki a matsayin likita a asibitocin gwamnati da kuma asibitoci masu zaman kansu. Sannan ya yi aiki a matsayin mataimakin firaminista a gwamnatin rikon kwaryar Libya . An nada shi mataimakin firaminista na farko a ranar 14 ga watan Nuwamba shekara ta 2012 zuwa majalisar ministocin karkashin jagorancin Ali Zidan . Abdulrahman ya kuma rike mukamin mukaddashin ministan cikin gida na wani lokaci. A ranar 29 ga watan Janairun shekara ta 2014 ya tsere daga wani yunƙurin kashe shi ba tare da rauni ba a cikin Tripoli .

Abdulrahman na wa’adin mataimakin firaminista ya kare ne a ranar 29 ga watan watan Agustan shekara ta 2014.