Sallar Idi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sallar Idi a Zehedan

Sallar Idi bikin daya ne na rana guda wanda duk dauka cin al'umma musulmai ke gudanar da da bukukuwa da shagali har da ziyarci ziyarci, sallar ido sallah ce, Wanda Allah ya shar'anta wa bayinsa a matsayinsa yayin kammala ibadah ta Azumin watan Ramadan.

Sallar Idi a Kaduna

Ban-bantar Sallar Idi[gyara sashe | gyara masomin]

Sallar Idi ba yinta a ke domin tunawa da wata ranar haihuwa ko wata nasara ko asara da aka samu ba ne. Sallar Idi ibada ce don yin godiya ga Allah.

Wasu abubuwa da ake son Musulmi ya yi Ranar Sallar Idi[gyara sashe | gyara masomin]

Mata a wurin sallar idi


Bayar da zakkar fidda-kai ga mabukata

Zakatul fitr wajiba ce kamar yadda Annabi Muhammad SAW ya farlanta ta. Ta fi falala a fitar da ita kafin a tafi masallacin Idi.

Amma an sawwaka a fitar da ita a daren Idi ko kwana biyu ko uku kafin ranar Idi, wato tun a ranar 27 na watan Ramadan musamman ga kungiyoyi ko wakilai da ke tattara zakkar domin raba wa mabukata.

Fitarwa da wuri zai taimaka zakkar ta isa ga mabukata da wuri kafin lokacinta ya wuce.

Annabi SAW ya ce: "Wanda ya fitar kafin Sallar Idi, to ya samu zakkar fidda kai. Wanda kuma ya fitar bayan idar da Sallar Idi to tana matsayin sadaka ne daga cikin ayyukan sadaka amma bai samu zakkar fidda kai ba."

Wankan zuwa Idi

Wankan zuwan Idi Sunnah ne. Ana son mutum ya yi wanka a ranar Idi kamar yadda yake wankan zuwa Juma'a.

Cin abinci kafin tafiya masallaci

Cin abinci kafin Idi Sunnah ce amma a Idin karamar Sallah (Idil-Fitr). Ana so mutum ya ci abinci kafin zuwa Idi domin koyi da Manzon Allah SAW.

Ba a so mutum ya jinkirta cin abinci a Idin karamar Sallah domin ka da ya nuna kamar ana azumi, domin rana ce da ba a yin azumi.

Malam ya ce Annabi SAW yana cin dabino kamar uku ko biyar ko bakwai ko tara kafin ya tafi sallar Idi. Amma a Idin babbar Sallah an fi so sai bayan an sauko Sallah.

Sanya tufafi masu kyau

Wannan al'ada ce da musulunci ya tabbatar da ita. Kuma sunnah ce ga musulmi ya saka tufafi sabo mai kyau.Tufafi na musamman, kuma ga maza an fi son ya kasance tufafi farare.

Idi ranar bayyana farin ciki ne da godiya ga Allah a kan ni'imar da ya yi wa bayinsa da dacewa da yin Azumi da ibadun da aka gudanar da kuma kyautar da ya samu na daren Lailatul Kadri.

Zikiri yayin tafiya zuwa masallacin Idi

Ana son a yi ta yin kabbarbari a yayin tafiya Idi har idan an zauna a filin Idi zuwa sai liman ya zo.

Mai tafiya Idi zai dinga cewa: "Allahu Akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar," ko kuma ya ce " Allahu Akbar, Allahu Akbar, Lailaha illahahu Wallahu Akbar, Allahu Akbar Walillahil Hamd.

Ana kuma cewa: "Allahu Akbar Kabira Walhamdu lillahi kasira, Wa Subhanallahi bukratan wa asila."

Za a daina kabbara idan Liman ya tayar da sallah.

Ba a sallar nafila a filin idi

Sallar Idi ba ta da Nafila domin ita ma Nafila ce. Amma idan a cikin masallaci ne za a yi Idi watakila saboda ruwan sama, to mutum yana iya nafilar gaisuwa ga Masallaci.

Amma a filin Idi ba a nafila. Mutum yana zuwa zai zauna kuma ya ci gaba da kabbara har isowar liman.

Sauraron huduba bayan sallar idi

Ana hudubar Idi bayan sallame Sallah. Ana son a zauna a saurari hudubar Liman, ba a son daga sallame sallah a fice.

Duk da cewa ba wajibi ba ne, amma malam ya ce yana daga cikin alherin da Annabi SAW ya yi nuni da shi domin samun albarkar addu'ar musulmi da ake yi a cikin huduba.

Sauya hanyar tafiya da dawowa

Wannan Sunnah ce ta Manzon Allah SAW, ba a son a tsayar da hanya daya. Ana son mutum ya sauya hanya idan zai dawo daga Idi domin zai yi wa wasu mutane na daban sallama sabanin wadanda ya yi wa sallama a lokacin tafiyarsa.

Yara, Mata, da tsoffi na zuwa Sallar Idi[gyara sashe | gyara masomin]

Ana son dukkan al'umma su tafi idi, maza da mata da yara da tsoffi. Mata masu haila za su iya zuwa amma ba za su shiga sahu ba, za su tsaya a gefen masallaci.

Ana son mata idan za su tafi idi su suturta jikinsu, ka da su tafi Ibadah suna bayyana jiki kuma suna bayyana adonsu. Sannan ba a son mata su jera sahu daya da maza a filin idi. An fi son maza suna gaba mata na baya.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

https://www.bbc.com/hausa/labarai-57079567

https://ha.m.wikipedia.org/wiki/Sallar_Idi_Babba