Jump to content

Samuel Aruwan

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Samuel Aruwan
Rayuwa
Haihuwa Kaduna, 10 Mayu 1982 (42 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a

Samuel Aruwan (an haifeshi ranar 10 ga watan Mayun shekarar 1982) ɗan jarida ne, kuma Kwamishinan Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna.[1][2][3]

Rayuwar farko da Ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

Samuel Aruwan ya fito ne daga Kabala West da ke Gundumar Tudun Wada, ƙaramar Hukumar Kaduna ta Kudu a Jihar Kaduna, Najeriya.[4][5][6] Shi kwararren ɗan jarida ne wanda yake da ƙwarewa shekaru goma kafin ya shiga aikin gwamnati a 2015.

Aruwan ya kammala karatun digiri a fannin sadarwa a kwalejin kimiyya da fasaha da ke Kaduna. A shekarar 2012, ya halarci horon horar da 'yan jarida na binciken Afirka a jami'ar Witwatersrand, Afirka ta Kudu. Ya kasance daya daga cikin ‘yan jaridar Najeriya da aka horar kan yadda za a dakile tsattsauran ra’ayin addini a Tony Blair Institute for Global Change, London a 2014 da kuma a Drew University’s Institute on Religion and Conflict Transformation, New Jersey in 2016.[7]

jarida da aikin gwamnati

[gyara sashe | gyara masomin]

Shi ɗan jaridane kwararre wanda yakai shekara goma da aiki kafin yafara aikin gwamnati a shekarar 2015[8][7]

  1. "Samuel Aruwan – Channels Television". Retrieved 2020-06-26.
  2. "Rebuilding intelligence gathering capacity of security forces". Daily Trust. Retrieved 24 June 2019.
  3. "El-Rufai appoints campaign spokesperson | Premium Times Nigeria". 2015-01-08. Retrieved 2020-06-25.
  4. http://www.citypeopleonline.com/meet-gov-el-rufais-tireless-spokesman/
  5. Msue, Aza (2019-07-03). "JUST-IN: el-Rufai Appoints His Spokesperson, Aruwan, 10 Others As Commissioners". Leadership Newspaper. Retrieved 2020-06-2
  6. "El-Rufai reappoints Samuel Aruwan , others – Invicta FM". Retrieved 2020-06-26.
  7. 7.0 7.1 "El-Rufai makes spokesman security commissioner". Punch Newspapers. 3 July 2019. Retrieved 2020-06-26
  8. Ndoma, Asabe (2019-05-15). "Meet Gov. EL-RUFAI's Tireless Spokesman - SAMUEL ARUWAN". City People Magazine. Retrieved 2020-08-24.

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]