Jump to content

Sansanin Vernon

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sansanin Vernon
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaGhana
Yankuna na GhanaYankin Greater Accra

Sansanin Vernon wani tsari ne na soja wanda aka tsara don sauƙaƙe kasuwancin bayi. Kamfanin Royal African Company ya gina sansanin a 1742 kusa da Prampram, wani gari a Yankin Greater Accra na Ghana. An gina shi da kayan arha - duwatsu masu kauri da swish. Danes ɗin sun lalata sansanin kafin 1783. Turawan Burtaniya sun sake gina ta a cikin 1806, amma ba da daɗewa ba ta fara rushewa kuma aka watsar da ita a kusan 1816. Turawan Burtaniya sun sake mamaye ta a 1831 amma an sake watsi da ita a 1844. Daga baya ya zama kango.[1]

  1. "Fort Vernon, Prampram". ghanamuseums.org. Ghana Museums and Monuments Board. Retrieved 17 July 2016.