Sarah Jibrin

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sarah Jibrin
shugaba

2017 -
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Sarah Jibrin yar siyasan Najeriya ce. Ita kadai ce macen da ta fito takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP.

Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Jibrin ta tsaya takara ne a zaben fidda gwani na Shugaban kasa na Jam’iyyar Demokradiyyar Jama’a a farkon shekarar 2011, to amma kawai ta samu nasarar jefa kuri’a daya daga cikin wakilai 5000.[1] [2]

Jibrin tayi aiki a matsayin mai bada shawara ta Musamman kan Halaye da Darajoji ga Shugaba Goodluck Jonathan. [3]

Ta kasance Shugaban kungiyar Justice Must Prevail Party (JMPP) na dan lokaci, wacce aka kafa a shekarar 2017.[3] Tana daga cikin shugabannin JMPP da suka yi rantsuwa a kan yaki hanci da rashawa a watan Yunin 2018.[4]

An shigar da ita a kyautar Hall of Fame na National Centre for Women Development.[5]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Sarah Jibril: When Women Betray A Woman, EConomic COnfidential, 1 February 2011. Accessed 20 May 2020.
  2. SARAH JIBRIN: My Defeat Will Haunt Womenfolk, P.M. News, 3 February 2011. Accessed 20 May 2020.
  3. 3.0 3.1 Fuse Democracy Day, handing-over day into Oct. 1, Jibrin tells FG, The Guardian, 16 June 2018. Accessed 20 May 2020.
  4. 2019: Ezeife, Sarah-Jibrin, Other JMPP Leaders Take Oath Archived 2020-11-15 at the Wayback Machine, Aljazirah, 14 June 2018.
  5. Nkechi Chima, Why we set up hall of fame for Nigerian women –Mary Ekpere-Eta, DG, Women Development Centre, The Sun, 1 March 2020. Accessed 20 May 2020.