Jump to content

Sardauna Memorial College

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sardauna Memorial College

Sardauna Memorial College (SMC) wacce aka fi sani da suna Sheikh Sabah College, Kaduna. Makarantar sakandari ce a kaduna wanda Sarkin Kuwait Sheikh Sabah Al-Ahmad Al-Jaber Al-Sabah ya kafa a jihar Kaduna yayin ziyara, bayan rasuwar Firayim Ministan Arewacin Najeriya Sir Ahmadu Bello makarantar ta canza sunan ta zuwa Sardauna Memorial College, ga abin da yake a yau kamar yadda Sardauna Memorial College (SMC). Ana gudanar da sallar juma'a a Massalacin Wanda kungiyar izala take daukar ragamar massalacin da gudanar da da'awa da dai sauran su.

Sardauna memorial collage
babban kofar shiga makarantar, ana cemata S M C.

Cibiyar Inshorar da Ma'aikata ta Najeriya wacce ake kira (NDIC) ta ba da gudummawar miliyan N24.9 na Kwalejin Sardauna Memorial (SMC) Kaduna, don samar da e-libarary.

Sheikh saba
masallacin dake cikin makarantar kenan

Tsofaffin daliban makarantar tana da wata kungiya da ake kira Sardauna Memorial College Old Boys Association, SAMOBA, Wadannan sunayen manyan mutane ne dasuka halarci makarantan

  • Ahmad Abubakar Gumi
  • Muhammadu Lawal Bello
  • Jika Dauda Halliru
  • Shehu Ladan
  • Usman Shehu Bawa
Wani bangare ne nan daga cikin makarantar

Daliban SMC ne suka fara cin gasar kwallon kafa na makarantun sakandare na duniya a ƙasar Finland.