Jump to content

Sawaba

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sawaba
Bayanai
Iri jam'iyyar siyasa
Ƙasa Nijar
Ideology (en) Fassara socialism (en) Fassara
Mulki
Shugaba Djibo Bakary
Hedkwata Nijar
Tarihi
Ƙirƙira 1956
Dissolved 1959

Hadakar Jama'a don Demokraɗiyya da Ci Gaba – Sawaba ( French: Union des Forces Populaires pour la Démocratie et le Progrès – Sawaba , UDFP – Sawaba) jam’iyya ce ta siyasa a Nijar, wacce aka kafa a matsayin Hadakar Demokradiyyar Nijar ( Union Démocratique Nigérienne, UDN) a shekarar 1954. Jam’iyya ta asali, wacce daya daga cikin shugabanin Jam'iyyar PPN wato Djibo Bakary ya kafa bayan an tsigeshi daga PPN, ta hada mambobi daga alhanzan Hausawa da kuma manoma daga gabashin Nijar. A wannan lokacin an sauya masa suna zuwa Mouvement Socialiste Africain – Sawaba. A yayin da ake kokarin samun cikakken 'yanci daga Faransa a zaben raba gardama na shekarar 1958, jam'iyyar ta wargaje sakamakon zagon kasa da aka yi mata bayan magudin da en mulkin mallaka sukayi mata. A lokacin samun 'yancin kai a shekara ta 1960 ta tsinci kanta cikin adawa kuma shugaban kasar Nijar na farko Hamani Diori ya sa an rufe jam'iyyar. Shugabanta wato Djibo Bakary dole ya yi hijira zuwa kasashe makwabta (Ghana, Mali, Guinea). Daga gudun hijira, jam'iyyar ta yi yunƙurin kamfen hambarar da mulkin Diori a cikin tsakiyar shekarar 1960s. A cikin shekara ta 1963-1964 wani yunƙurin juyin mulki wanda ya biyo bayan wani harin tawaye a kan iyakokin Nijar ya haifar da tashin hankali a Yamai, duk da cewa harin na gaba da gaba ne. Shugabancin Jam'iyyar ya koma Nijar biyo bayan juyin mulkin soja na shekarar 1974, amma ba da daɗewa ba aka kame mafi yawan shugabanin ta kuma aka sa wasunsu barin kasar, wasu kuma an mayar da su saniyar ware. Bayan dawowar mulkin dimokiradiyya a shekarar 1991, Bakary wanda yanzu ya tsufa ya sake kafa jam’iyyar a matsayin UDFP – Sawaba. A cikin zaɓen shekara ta 1993 ya kuma sabo kastantancen sakamako wanda bai ma kai kashi biyu cikin dari ba. A tsakanin shekarar ne jam’iyyar ta rabu, inda wani sabon bangare (UDFR – Sawaba) ya shiga cikin hadakar gwamnati tare da tsohuwar abukiyar hamayyarsu wato PPN. Duk da mutuwar Bakary a 1998 da kuma ci gaba da rashin nasarar zabe, bangarorin biyu masu rike da sunan Sawaba suna ci gaba kasancewa cikin siyasar Nijar.[1][2]

  1. Decalo, Samuel (1997), Historical Dictionary of Niger African Historical Dictionaries, ebook ISBN 9780585070087, p.58-60
  2. Fuglestad, Finn (1973). Djibo Bakary, the French, and the Referendum of 1958 in Niger, Cambridge University Press, vol. 14, No:2, pp.313-330, http://www.jstor.com/stable/180451