Jump to content

Sihem Amer-Yahia

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sihem Amer-Yahia
directeur de recherche (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Aljir, 1972 (51/52 shekaru)
ƙasa Aljeriya
Karatu
Makaranta University of Paris-Sud (en) Fassara
Ecole Nationale Supérieure d'Informatique (en) Fassara
Paris Dauphine University (en) Fassara
Institut National de Recherche en Informatique et en Automatique (en) Fassara
Thesis director Claude Delobel (en) Fassara
Sana'a
Sana'a computer scientist (en) Fassara da researcher (en) Fassara
Kyaututtuka

Sihem Amer-Yahia kwararriya ce 'yar ƙasar Aljeriya ce masaniyar kwamfuta. Ita ce Daraktan Bincike na CNRS a Laboratoire d'Informatique de Grenoble. Tana jagorantar ƙungiyar bincike ta SLIDE.[1] Sihem Amer-Yahia tana aiki akan sarrafa bayanai,[2] yaruka n bayyanawa da algorithms na sarrafa tambaya. Abubuwan da ta wallafa sun haɗa da crowdsourcing, computational complexity, data analysis, data handling, data visualisation, information science, da magance sabbin matsalolin sarrafa bayanai a cikin intanet masu zuwa da manyan aikace-aikacen bayanai.[3]

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]
Hutun Sihem Amer-Yahia

Amer-Yahia ta sami Ph.D. a CS daga Paris-Orsay da INRIA a cikin shekarar 1999, [4] da Diplôme d'Ingénieur daga INI, Algeria.

Kafin ta shiga CNRS, Amer-Yahia ta yi aiki a matsayin Babbar Masaniyar Kimiyya a QCRI, Babbar Masaniyar Kimiyya a Yahoo! Research da Memba na Ma'aikatan Fasaha a AT&T Labs.[5]

Amer-Yahia tayi aiki a kwamitocin jaridu da dama ciki har da kwamitin zartarwa na SIGMOD. Tana ɗaya daga cikin amintattun Kyautar VLDB.[6]

Amer-Yahia kuma ta yi aiki a Hukumar EDBT (Extending Database Technology), kuma ita ce shugabar kwamitin shirye-shirye na taron EDBT a shekarar 2014. Ita ce Babbar Editan Jaridar VLDB na Turai da Afirka.[7]

Ta kasance editan haɗin gwiwa na ACM TODS, lokacinta yana ƙarewa a cikin shekarar 2017, kuma ta kasance editan yanki na Jaridar Systems Systems. [8]

Kyaututtuka da karramawa

[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin shekarar 2020, Amer-Yahia ta sami Medal Azurfa na CNRS.[9]

A cikin 2017, an gane Amer-Yahia a matsayin fitacciyar memba na ACM.[10]

  1. "Sihem Amer-Yahia | Laboratoire d'Informatique de Grenoble" . Retrieved 2020-03-08.
  2. "BICOD 2017" . www.dcs.bbk.ac.uk . Retrieved 2020-03-08.
  3. "Sihem Amer-Yahia as an IEEE author" . Retrieved 2020-03-08.
  4. Amer-Yahia, Sihem (1999-01-01). Du chargement en masse dans une base de donnees (en general) et de la migration relationnel-objet (en particulier) (thesis thesis). Paris 11.
  5. "Sihem Amer-Yahia - Home" . dl.acm.org . Retrieved 2020-03-08.
  6. "Board of Trustees" . www.vldb.org . Retrieved 2020-03-08.
  7. "The VLDB Journal" . Springer. Retrieved 2020-03-08.
  8. Information Systems Editorial Board .
  9. "Médailles d'argent 2020 | CNRS" (in French). CNRS. 13 February 2020. Retrieved 2020-03-08.
  10. "Sihem Amer-Yahia" . awards.acm.org . Retrieved 2020-03-08.